Ga al'umma: "KU YI AMFANI DA DARUSSAN DA AZUMIN RAMADAN YA KOYAR - Sarkin Alhazan Katsina

Ga al'umma: "KU YI AMFANI DA DARUSSAN DA AZUMIN RAMADAN YA KOYAR - Sarkin Alhazan Katsina 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Anyi kira ga al'ummar musulmi da su dauki darussan da suka koya acikin watan azumin Ramadan don yin aiki da su, musamman akan abin da ya shafi zaman lafiya,hakuri da juriya, sada zumunci tare da ci gaba da yiwa shugabanni da kasa baki daya addu'o'in samun nasara tare da karuwar arziki.
Sarkin Alhazai na Katsina wanda kuma yake shi ne shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta Jahar Alhaji Kabir Bature ne yayi wannan kira daga can kasa mai tsarki wajen aikin Umra da yaje, a sakon da ya aiko na barka da shan ruwa ga al'ummar jahar sakon da wakilin mu ya ci karo da shi ta hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar jin dadin alhazan Alhaji Badaru Bello Karofi. Sarkin Alhazan wanda yace, duk da cewa ranar Laraba ce zata zamo ranar bukukuwan salla karama domin rashin ganin jinjirin watan Shawwal da ba'a yi, ya ja hankalin jama'a da su cigaba da yin hakuri akan kowane irin al'amari musamman akan abin da ya shafi addini ba ma kamar a irin wannan lokaci wanda ake ganin kusan anyi azumin cikin wani yanayi maras kyau, ga tsadar rayuwa ga kuma tsananin zafin ranar da aka fuskanta a daidai ranakun da watan ke shirin yin bankwana.
Shugaban hukumar har ila yau, ya qara jadda manufa da kuma qudurorin gwamnatin Malam Umar Dikko Radda akan kawo abubuwan alheri ga al'ummar jahar. Ya kara da cewa, mahajjatan da zasu sabke farali a bana da su sani cewar gwamnatin jahar tayi tsari mai kyau tare da tanadar masu duk wasu abubuwan jin dadi ta yadda zasu gudanar da aikin ibadar ba tare da shiga cikin wata damuwa ba duk kuwa da irin kalubalen da aikin na 2024 ya zo da shi, wannan kuma ba wani abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da cewa, duk shekara akwai irin nau'in matsalar da aikin yake zowa da ita, a addinance ma an ga haka. "Mu ci gaba da yin addu'o'in samun zaman lafiya a tsakanin mu, Jahar mu da kuma kasar mu baki daya, domin ita ce maganin komi", inji Shugaban kuma Sarkin Alhazan na jahar Katsina Alhaji Kabir Bature. 

Post a Comment

Previous Post Next Post