Faduwar dala: ZA'A IYA MAYAR DA RARAR KUDIN MANIYATAN HAJJIN BANA - NAHCON

Faduwar dala: ZA'A IYA MAYAR DA RARAR KUDIN MANIYATAN HAJJIN BANA - NAHCON 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
    Shugaban NAHCON Alhaji Jalal A. Arabi
Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyatan aikin Hajjin 2024 da rarar kuÉ—in da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.
Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X(Twitter) ranar Alhamis.
"Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1,000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuɗinka ta dawo naira 900, to ai ka ga akwai rarar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata mu mai da maka. Ba mu jira tana ta yin ƙasa ba. To idan kuma ta ƙara yin sama fa?" In ji Jalal Arabi.

Alhaji Arabi ya kara da cewa "indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan haƙƙin kowa ba da izinin Allah. Za mu tabbatar mun biya kowa wannan rarar kudin
To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya bai faÉ—i lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuÉ—aÉ—en nasu ba.
A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaÉ—en ne bayan kammala aikin Hajji.
A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka.

Post a Comment

Previous Post Next Post