ANYI KIRA GA MANIYATAN JAHAR KATSINA DA SU CI GABA DA HALARTAR TARON BITA DON SANIN YADDA AKE AIKIN HAJJ - Sarkin Alhazai
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Shugaban hukumar alhazai na jahar Katsina wanda kuma shi ne sarkin Alhazan Katsina Alhaji Kabir Yusuf Bature yayi kira ga maniyatan jahar Katsina sama da dubu biyu da zasu sabke farali a wannan shekara ta 2024 da su ci gaba da halartar wuraren dake taron bita don sanin yadda ake aikin Hajji da a halin yanzu ake cigaba da yi a shiyyoyin hukumar dake fadin jahar.
Shugaban hukumar wanda Sheikh Goni Dokta Muneer Ja'afaru ya wakilta a wajen bude taron bitar na wannan shekara wanda kuma yace, wannan sako na shi ya ci gaba da aiki har sai ranar da aka ce an gama kwaahe maniyatan jahar zuwa ƙasar Saudi Arabia, inda ya baiyana cewar, ita wannan bitar tana kara fadakar da maniyata tare da ilmantar da su abubuwa da dama da suka shafi wannan aiki na ibada wanda kuma duk shekara ya kan zo da wasu sabbin sauye-sauye, matsaloli da kuma tsare-tsare wadanda in maniyaci bai san da su zai iya fuskantar matsalar da ka iya janyo yayi hasarar aikin baki daya. Sarkin Alhazan wanda ya jinjinawa Gwamna Radda ta irin yadda gwamnatin shi ta dauki nauyin wasu mutane domin ganin cewa an gudanar da aiki karbabbe. "An dauko masu wa'azi mutun bi-biyu mace da namiji daga kowace karamar hukuma da kuma matakin jaha. Akwai masu kula da kiwon lafiya baya ga jagorori da sauran irin su da gwamnati ta dauki nauyi don ganin maniyatanmu basu yi asarar makudan kudaden da suka biya don sabke wannan farali. Kazalika, akwai ma wani shiri na musamman a bangaren abinci inda aka kebe abincin masu lalura. Sannan ga masabkai masu kyau kuma kusa da Harami. Don haka babu abinda za'a ce sai godiya ga Allah".
Shugaban hukumar bai tsaya anan ba sai da ya nemi maniyatan da su ci gaba da yiwa jahar addu'o'in samun zaman lafiya da ci gaban arzikin ta a duk lokacin da suke yin addu'o'i a can kasa mai tsarki. Da ya juya ga sashen ma'aikatan hukumar, Sarkin na Alhazai ya jinjina masu ta irin yadda suke gudanar da aiyukan su ba tare da nuna gajiya. Har'ila yau, ya kara jinjinawa tare da yabawa Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama wanda yace, jajircewar shi ta sa aka kai ga halin da ake ciki na cimma wasu nasarorin aikin da za'a iya anci kashi 50 ko ma fiye da haka acikin kashi 100.