KAKAKIN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA YA ZAMA UBAN GIDAUNIYAR TALLAFAWA MABUKATA

KAKAKIN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA YA ZAMA UBAN GIDAUNIYAR TALLAFAWA MABUKATA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Bayan karramawar da ta yi ma shi, gidauniyar tallafawa mabukata mai suna "Kabir Idris Omega Charitable Foundation" dake da mazauni a garin Dandagoro ta karamar hukumar Batagarawa dake cikin Jahar Katsina, har ila yau, gidauniyar ta nada shi Kakakin hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Badaru Bello Karofi a matsayin uban ita wannan gidauniya.
Kamar yadda shugaban gidauniyar Salisu Karama yace, membobin wannan gidauniya sun lura da irin aiyukan da Alhaji Badaru ke yi musamman na taimakawa marayu da sauran mabukata ta hanyoyi da dama acikin garin na Dandagoro, jaha da kuma a can kasa mai tsarki a lokacin da ake gudanar da aikin Hajji.
Shugaban ya kara da cewa, "Alhaji Badaru mutun ne wanda yasan darajar mutane kuma baya kyamar kowa. Sannan mutun ne wanda yake kokarin ganin ya hana matasan mu yin zaman banza ta hanyar basu shawarar su nemi na kansu sannan su guji shiga cikin mugayen halaye musamman na tu'ammali da miyagun kwayoyi".
Bayan karbar takardar bashi wannan matsayi, Alhaji Badaru Bello Karofi yayi godiya akan wannan karramawa tare kuma da bashi wannan matsayi. A cikin takaitaccen bayanin da yayi,uban gidauniyar yace, bashi da abin da zai ce masu illa fatan alheri da kuma alkawalin cigaba da bayar da gudunmuwa tare da yi masu jagoranci a inda suke ganin basu iya. Karshe yayi fatan alheri ga ita wannan gidauniya tare da yin kira ga jama'a da su rika shiga a irin wadannan kungiyoyi domin bayar da tasu gudunmuwar. 

Post a Comment

Previous Post Next Post