HUKUMAR KWASTAM TA MAYAR DA MANYAN MOTOCI 6 NA HATSI DA AKA KAMA GA MASU SU A KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumar hana fasa kwabri da aka fi sani da kwastan a jihar Katsina ta mika manyan motoci guda shida da aka kama dauke da nau’in hatsi iri iri ga masu a jihar kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni.
Wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun Kakakin hukumar na jihar Sufeto Tahir Balarabe tace,an mika hatsin ga masu hannun jarin a hedkwatar Kwastam Katsina a wannan Laraba 13 ga Maris, 2024. Kwanturola na yankin, Mohammed Umar, ya ce sakin hatsin da aka yi ga masu shi ya biyo bayan bin umarnin shugaban kasa.
Tun da farko rundunar shiyyar hadin guiwa da na tarayya ta shiyyar B ta kama wasu manyan motoci guda shida (6) a ranar 18 ga watan Fabrairu, 2024 dauke da buhunan hatsi iri-iri a kan hanyar Kwanar Gwanti, Dogon Hawa a bisa hanyar zuwa karamar hukumar Mai'aduwa ta jihar. su kasance kan hanyarsu ta ficewa daga kasar.
Kwanturola Umar ya kara da cewa, shugaba Tinubu ya umurci hukumar kwastam ta Najeriya da ta mayar wa masu hatsin da suka kama bisa sharadin cewa za a sayar da shi a kasuwannin Najeriya domin tabbatar da wadatar abinci da kuma rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta a baya-bayan nan.
Don tabbatar da bin ka’ida, ya bayyana cewa rundunar tare da hadin gwiwar jami’an leken asiri na Kwastam (CIU), da sashen kula da harkokin tsaro na tarayya (FOU B), da kuma jami’an tsaro na hadin gwiwa (JBPT), za su sanya ido kan yadda ake sayar da hatsin da aka saki don tabbatar da cewa ba a fitar da shi daga kasar ba.
Kazalika, Kwantarolan ya kara da cewa ma’aikatar karkashin jagorancin CGC Bashir Adewale Adeniyi MFR da tawagarsa sun himmatu wajen samar da kyakkyawar tattaunawa da hadin gwiwa da al’ummomin kan iyaka domin tabbatar da tsaro da samun wadata a kasar nan.
Kwanturola Umar ya ce: “Bisa umarnin babban kwamandan sojojin kasa, Bola Ahmed Tinubu GCFR na sakin duk wani nau’in hatsi da ke hannun hukumar kwastam ta Najeriya, a yau mun mika manyan motoci guda shida da abubuwan da suke dauke da su ga masu shi.
“Hukumar CGC a ziyarar aiki da ya kai Katsina, ta bi umarnin shugaban kasa, wanda ya ba da umarnin mayar da kayan abincin da aka tsare ga masu shi da sharadin cewa za a sayar da su a kasuwannin Najeriya.”
Ya jaddada cewa: "Martanin umarnin shugaban kasa shine tabbatar da samar da abinci da kuma rage wahalhalun da ake fuskanta a kasar."
Sai dai ya yi kira ga jama’a da su bayar da sahihan bayanai ga hukumar kwastam ta Najeriya da za ta taimaka wajen dakile safarar kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki daga kasar zuwa ketare.
Da yake karbar kayayyakin a madadin masu shi, shugaban karamar hukumar Mai’adua, Hon. Salisu Mamman NaAllah, ya nuna godiya ga shugaban kasa bisa wannan karimcin da aka yi masa, ya kuma ba da tabbacin cewa, masu wannan hatsin da aka sako za su bi umarnin shugaban kasa.
Daga nan sai ya mika godiyarsa ga Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam bisa ziyarar da ya kai a Mai’adua a kwanan baya da kuma yadda ya mayar da martani ga koke-kokensu da suka yi, sannan ya yaba wa kokarin Shugaban Hukumar Kwastam na Katsina kan kyakkyawar alakarsa da al’ummar yankin.