Hajj2024: SASHEN GUDANARWA, ZARTASWA NA HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA ZA SUYI AIKI TARE DON SAMUN NASARAR AIKIN- Shugaba
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya nuna damuwar shi akan irin matsalar da ta kunno kai a abinda ya shafi aikin Hajjin wannan shekara ta 2024 musamman akan batun wani irin tashin gwabron zabon da kudin kujerar aikin ta yi a inda masu tsohuwar ajiya zasu yi cikon kusan naira milyan biyu yayin da sabbi zasu biya sama da naira milyan takwas, abin da bai yiwa maniyatan da sauran musulmi dadi ba, duk kuwa da irin yadda ita hukumar kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON ta baiyana dalilan faruwar hakan.
Gwamna Radda,ya baiyana rashin jin dadin ne a satin da ya gabata a lokacin da yake kaddamar da sashen gudanarwar (Board members) hukumar a gidan gwamnatin Jahar,kamar yadda wani rahoton da ya fito daga ofishin jami'in hulda da jama'a na hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Badaru Bello Karofi ya fitar. Gwamna wanda yayi dogon bayani akan abin da ya shafi aikin na Hajji da kuma nauyin da ya rataya akan su shugabannin, har ila yau, ya shawarce su da su rike amanar da aka damka masu musamman ganin cewa, aiki ne na ibada zasu kula da shi. Hakan na da nufin sai sun hada hannu wuri guda tare da sauran sashen zartaswa da sauran ma'aikatan hukumar za'a iya samun nasarar gudanar da aikin musamman lura da irin kalubalen da aikin yake tattare da shi.
A nashi jawabin, Shugaban hukumar jin dadin alhazai na jahar Katsina wanda kuma shi ne sarkin Alhazan Katsina Alhaji Kabir Bature ya shaidawa Gwamna Malam Umar Dikko Radda cewa, sassan hukumar biyu, na gudanarwa da na zartaswa zasu yi aiki tukuru kuma a matsayin tsinya mai madauri guda domin ganin cewa, Jahar tasu nasarorin da ake bukata a wajen gudanar da aiyukan Hajji mai zuwa na wannan shekara ta 2024.
Sarkin Alhazan ya shaidawa Gwamnan cewa, tuni sassan biyu ke tuntubar juna domin ganin cewa ana cigaba da tsare-tsaren da suka dace domin ganin cewar jahar ta ci gaba da rike kambinta na samun nasara a duk lokacin da aka je wannan aikin ibada. Shugaban hukumar, ya kara jaddada goyon baya tare kuma da bin duk wani tsari da gwamnatin jahar zata kawo domin ganin cewa, an samu cin nasarar aikin. Kazalika, yayi kira ga sauran abokan aikin shi da cewar, su sani nauyi ne wanda Allah ya aza masu ta hannun shi Gwamnan wanda kuma za'a yi masu tambayoyi akan yadda suka gudanar da shi a ranar da babu mai magana sai wanda aka tambaya.
Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai ya kuma mika godiyar su ga Gwamna Malam Umar Dikko Radda bisa ga yadda yaga cancantar su ya zabo su ya dora masu wannan nauyin da ya fi kowane nauyi nauyi saboda magana ce wadda ta shafi addini.