GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA HAƊA HANNU DA HUKUMAR RAYA ƘASASHE TA MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA DOMIN GINA GIDAJE 140 GA 'YAN GUDUN HIJIRA

GWAMNATIN JAHAR KATSINA TA HAƊA HANNU DA HUKUMAR RAYA ƘASASHE TA MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA DOMIN GINA GIDAJE 140 GA 'YAN GUDUN HIJIRA 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka, Katsina 
Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da shirin haɗa kai da hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP domin gina gidaje kusan xari da arba’in ga 'yan gudun hijira. Gwamnatin ta bayyana hakan ne a ƙoƙarin da ake na magance matsalar ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Jibia da ke jihar.
 Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda ne ya tabbatar da hakan a yayin ziyarar da tawagar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa, karkashin jagorancin kwamishinan gwamnatin tarayya, Tijjani Aliyu Ahmed.
Kamar yadda sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Malam Ibrahim Kaula ya sanyawa hannu tace, Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samar da filayen da suka dace domin aikin gina gidajen tare da shirin samar da shinge da ababen more rayuwa a wani bangare na gudunmuwar takwararta.
"Gwamnatin jihar ta kuduri aniyar rage yawan sansanonin ‘yan gudun hijira ta hanyar baiwa mazauna yankin horon sanin makamar aiki,” in ji Gwamna Radda. Ya kuma jaddada muhimmancin baiwa ‘yan gudun hijira sana’o’in hannu domin saukaka shigarsu cikin al’umma tare da kafa nasu sana’o’in idan sun koma garuruwansu.
Bugu da kari, Gwamna Radda ya bayyana shirye-shiryen shirin horarwa tare da hadin gwiwar abokan ci gaban jahar don tallafawa 'yan gudun hijirar. 
Da yake nuna jin dadinsa kan tallafin abinci da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa ta bayar, Gwamna Radda ya bayyana bukatar samar da cibiyar ‘yan kasuwa a yankin Arewa maso Yamma, inda ya bukaci a kula da jihar Katsina saboda yadda hukumar bunkasa sana’o’i ta ke da shi.
A martanin da kwamishinan gwamnatin tarayya, Tijjani Aliyu Ahmed ya mayar, ya jaddada damuwar gwamnatin tarayya kan ayyukan ‘yan bindiga a jihar. Ya yabawa gwamnati da al’ummar jihar Katsina bisa yadda suka mayar da martani kan kalubalen da ‘yan gudun hijira ke haifarwa.
 Kwamishina Aliyu Ahmed ya bayyana shirin samar da cibiyoyin koyar da sana’o’i a shiyyoyin siyasar kasa uku na Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, da Arewa ta Tsakiya. Wannan yunƙurin na nufin ba wa IDP kayan aiki masu dorewa don dogaro da kai da kuma rage dogaro ga wuraren sansanin.
Hukumar ta kuma kai wani kaso na kayan abinci don tallafawa kimanin ‘yan gudun hijira dari bakwai da aka gano a jihar.Yunkurin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina, UNDP, da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta kasa, ya nuna aniyar rage wahalhalun da ‘yan gudun hijirar ke fuskanta tare da samar da mafita mai dorewa don sake dawo da su a cikin al'umma tare da karfafa musu gwiwa.


Post a Comment

Previous Post Next Post