ALLAH NE YA TSINEWA MASU ƁOYE KAYA DON SUYI TSADA - Goni Muneer

ALLAH NE YA TSINEWA MASU ƁOYE KAYA DON SUYI TSADA - Goni Muneer

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Matashin malamim addinin Musuluncin nan dake garin Katsina Sheikh (Dr.) Goni Muneer Ja'afaru ya baiyanawa cewa, Allah ne ya tsinewa masu ɓoye kayan sayarwa da nufin sai sunyi tsada sannan su fiddo su sayar.
Malamin ya baiyana haka ne a wajen buɗe tafsirin azumin wannan shekara ta 2024 a Zawaiyar Maulana Sheikh Ibrahim Sale gidan Dawa Katsina a ranar litinin 1 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 11 ga watan Maris, 2024.
Sheikh Muneer a wata doguwar tunatarwa tare da nasihar da ya yiwa al'ummar musulmi, ya kuma ja hankalin musamman 'yan kasuwa tare da sauran masu dabi'ar sayen wani abu su boye don yayi tsada su fiddo su sayar bama kamar a cikin wannan wata mai albarka. Ya kara da cewa, "sai kaga dan kasuwa yana ta rantsuwa akan karya game da farashi harma ya rika nuna cewa shi fa yana azumin, amma yana fadin haka ne bisa karya don kawai a yarda da shi amma ba don gaskiyar lamarin ba ne. Addini ya koyar da irin yadda ake cin riba ga harkokin kasuwanci amma ba irin wanda ake yi na yanzu ba". Sheikh Goni ya kawo ayoyi da hadisan Manzon Tsira akan wadanda suke kuntatawa bayin Allah da irin sakamakon da zasu samu a ranar Yaumul Tublar Sara'ibu.
Akan haka malamin, ya roki al'umma da su taimakawa mabukata koda kuwa da dabino ne kamar yadda ya zo a wata ruwayar. "Kyautata na daga cikin aiyukan da Allah madaukakin sarki ke bayar da ladarsa maras adadi musamman a irin wannan yanayi da kuma watan mai albarka. Sannan jama'a su kiyayi kirawa kansu masifa da kansu, domin Allah zai horewa mutun abu amma ya rika kiran babu, to sai Allah ya dauke abin da ya baka ya barka da babun". Malamin wanda acikin jawabin nashi ya tunatar da cewa, a ci gaba da tafsirin Al-Ƙur'ani mai girma, za'a tashi ne daga inda aka tsaya a bara, wato, kissar Annabi Yusuf acikin suratul Yusuf wadda ke dauke da darussan kalubalen rayuwa iri-iri. 

Post a Comment

Previous Post Next Post