MATASA ZASU IYA RIQE SIYASAR WANNAN ZAMANI - Nasiru Tarkama

MATASA ZASU IYA RIQE SIYASAR WANNAN ZAMANI - Nasiru Tarkama 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Wani matashin dan siyasa Alhaji Nasiru Tarkama ya ce, hakika matasa zasu iya rike siyasar fiye da lokuttan baya. Alhaji Nasiru ya kara da cewa, "yanzu ne maganar da ake yi ta cewa matasa sune kashin bayan ci gaban al'umma take tabbata musamman a jahar Katsina. Alhaji Nasiru ya baiyana haka ne a wata tattaunawar da suka yi da wakilin mu a Katsina.
"Ai batun cewa matasa na iya rike wannan siyasar abin a fili yake saboda shekera da shekaru ana jaraba tsofaffin amma basu tsinana komi ba. Gwamnan mu na yanzu Malam Umar Dikko Radda yayi abin da wadancan basu yi tunani a kai ba. Irin abubuwan dake faruwa na cigaba a jahar ba sai ance komi ba domin abu ne a fili. Cikin watanni bakwai a bisa mulki abin da yayi ya fi na shekaru hudun da wasu suka yi. Irin wannan rawa da ya fara takawa ya nuna cewa matasa na iya rike shugabanci tun daga na Kansila har zuwa na shugaban kasa".
Matashin yayi bayani mai tsawo tare da kawo misalai iri-iri wadanda ke nuni da cewar matasa zasu iya rike siyasa da kuma mukamanta ta fuska dabam-daban. "Mu dubi Gwamnan Zamfara da Kano. Anan jahar Katsina idan ka dubi matakan tsaron da ya dauko a yanzu ka duba can baya, yaya abin yake? Babu wanda yayi tunanin kawo hanyar da Gwamna Malam Umar Dikko Radda ya kawo. A Kano suna cewa idan gwamnatin su zata yi shekara hudu, to sai an fidda labarin waccan gwamnatin da ta shude. To bare mu anan jahar Katsina wanda idan muka yi shekara hudun, to sai ma an mance kakaf cewar anyi wata gwamnati a baya face wannan. Maganar gaskiya a yanzu ne ta yaro take yin kyau da Æ™arko. 
Matashin wanda yace, cikin wadancan shekaru da aka yi ga batun tsaro wanda abin ya kai ga rashin samun bakin zaren sai ga shi yanzu harma warwarar ake yi ta fuska biyu. Fuskar farko batun shawo kan matsalar tsaron sannan ga samawa matasa aikin yi. Sannan ga tsare-tsare ta fuskar ilmi wanda a tarihin jahar Katsina ba'a samu lokacin da aka dauki matasa koda dubu daya aiki ba, amma sai ga shi Gwamna Radda   ya dauki malaman makaranta kuma matasa sama da dubu bakwai a lokaci guda. Kamar ma yadda muke jin wasu labaran, kafin wannan gwamnati ta gama shekaru hudun ta sai ta dauki malamai sama da dubu 15.
Shin malam Nasiru yana nufin yanzu a jahar Katsina ba batun bambancin siyasa ake yi ba an koma ga matasa? "Wannan tabbas haka abin yake. Ka dubi irin nade-naden da yayi, ai kashi 85 zuwa 90 ai matasa ne. Sannan mutane wadanda anyi karatu an gogu dan ingiji suke nema don su bayar da tasu gudunmuwar, to sai ga wannan damar. Wata 'yar hirar da nayi da Kwamishinan kasa da sufuyo irin tsare-tsaren da yayi mani bayani akan yadda za'a mayar da jahar ba wai garin ba ta hanyar cigaban hanyoyi da gine-gine, ko kasar turai aka yi haka sai kallo. Akwai batun yin gidaje, hanyoyi da sauran su. In koma baya, idan ka tuna lokacin da akayi wannan mukabala ta kafin a zabe su, ya gayawa abokan takarar shi cewa, idan Allah ya bashi mulkin to zai janyo su domin a yiwa jaha aiki, haka su ma, duk wanda Allah ya ba zai bi shi domin su ciyar da jahar gaba domin dukkan su suna yi ne don kawo cigaban jahar ga shi kuma haka ake a yanzu. A bincika a ji, akwai 'yan PDP acikin wannan gwamnati kuma suna rike da wasu mukaman. A takaice, irin salon marigayi Malam Umaru tsohon shugaban kasa yake bi. Hatta da can matakin kasa haka abin yake. "To bari in gaya maka, idan da Gwamna zai ga cewar dan jam'iyarsa ba zai iya yin wancan abu ba, sai yaga dan jam'iyar adawa ne zai iya, to ina tabbatar maka da cewar wancan na adawar zai ba domin anyi mun gani ko a yanzu cikin masu rike da mukaman. Bugu da kari, matasanmu na karkara ba'a bar su a baya ba, anyi rejistarsu ta hanyar Mai baiwa Gwamna shawara akan matasa yayi domin ganin cewa an dama da su. Ga batun noman rani wanda tuni har an kawo kayan aikin an kuma ba matasan. Yanzu yaushe rabon da kaji matasan na kukan cewa an bar su baya?
Malam Nasiru Tarkama yace, idan aka lura, su fa matasa a kullum ina zasu bada tasu gudunmuwar suke nema ba ina zasu samu kudin da zasu tara ba kamar yadda mafi yawan dattawa ko tsaffin ke yi. Saboda haka, ya kara jaddada cewar wannan karnin na matasa ne wanda kuma zasu yi iya yin su na ganin sun bayar da duk wata gudunmuwar da zata kawo cigaba. Saboda haka, yayi kira gare su da su sani cewar a yanzu suna bisa wani ma'auni ne wanda idan suka cika mudu a sake neman awon su ko kuma su samu akasi idan suka gaza. 

Post a Comment

Previous Post Next Post