Hajj 24: BAYAN CIKA KA'IDA ZA'A YI BIKIN BAJE KOLIN MANIYATAN DA SUKA SAMU BIZAR ZUWA AIKIN HAJJIN BANA A JAHAR KATSINA - Hukuma

Hajj 2024: BAYAN CIKA KA'IDA ZA'A YI BIKIN BAJE KOLIN MANIYATAN DA SUKA SAMU BIZAR ZUWA AIKIN HAJJIN BANA A JAHAR KATSINA - Hukuma

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
  

An ja hankalin maniyatan jahar masu son sabke farali a wannan shekara ta 2024 da suyi kokari su cika sauran ka'idodin da suka rage kafin ranar 1 ga watan Maris. Sauran ka'idojin da suka rage sune, tabbatar da cewa ga wadanda suka biya kudaden su daidai na naira milyan 4 da dubu dari 6 da 99 amma basu kawo fasfo nasu ba da suyi hanzarin kawowa kafin ranar 1 ga watan Maris lokacin da hukumomin Saudiya zasu fara bayar da biza ga masu zuwa aikin Hajjin.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama shine ya sanar da haka a yau talata a wata hira da manema labarai da yayi a ofishinsa dake cikin harabar hukumar acikin garin Katsina. Dankama wanda har ila yau, ya sake yin kira ga maniyatan da suka fara ajiye kudin su na naira milyan 3 da rabi da suyi hanzarin cika sauran kafin waccan rana sannan kuma kawo fasfunan nasu ga ofisoshin hukumar da suka bayar da kudaden nasu domin samar da waccan bizar, in kuwa don sun bayar da wadannan kudade kuma suna takamar sun kawo fasfo to su sani suma basu da bizar saboda basu cika kudin ba. Daraktan ya kara da cewa, rashin cika wadancan ka'idojin zai sa maniyatan ba zasu samu iznin shiga kasar ta Saudiyya balle sabke faralin.
Tun farko sai da Daraktan ya fara shaida irin nasarori da tsare-tsaren da hukumar take yi tun daga lokacin da Gwamna Radda ya bashi jagorancin ta kimanin watanni biyu zuwa uku da suka wuce, inda yace, "zamu yi tsarin da kowane maniyaci yasan halin da ake ciki. Babban aikin da suke cikin yi shine yiwa maniyatan rejista, domin in ba'a manta ba, Jahar ta samu kaso na yawan kujeru dubu 4 da dari 5. A halin yanzu mun amsi kudi sama da kashi 50 cikin dari na maniyatan da suka biya ko aka yiwa rejista daga cikin wancan adadin yawan kujerun da aka bamu". Saidai Daraktan yace, batun karbar sabbin biyan kudin kujerar tuni aka rufe saidai na masu ajiyar da suka rage ne muke kira gare su da suyi kokarin cikawa tare da kawo fasfo na su kamar yadda na ambata. Hukumar Saudiyya tayi tsari mai kyau ta yadda suka shirya fara bayar da bizar daga ranar 1 ga watan Maris har zuwa tsawon sati uku. Sannan za'a yi bikin baje kolin maniyatan da suka samu bizar walau a shiyyoyinsu da kuma hedkwatar. 
Kazalika, Alhaji Yunusa ya kara da cewa, hatta da zuwa kasa mai tsarki domin kamawa maniyata masabkai da batun abinci da sauran su, wannan hukuma taje karkashin hukumar dake kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON bayan amincewa shi Gwamna Malam Umar Dikko Radda. Babban Daraktan ya ci gaba da cewa, kamar yadda aka sani, ita hukumar alhazai ta Saudiyya da hukumar kula da aikin Hajji ta kasa take hulda kai tsaye su kuma suyi da jihohi. To tun kafin zuwan mu wancan aiki na neman masabkai, sai da Maigirma Gwamna Radda ya kafa wani kwamiti wanda yayi nazarin rahoton aikin 2023 inda suka bayar da wasu shawarwari har 34 wadanda suka hada da batun fitar da fannin nau'in abinci na musamman ga wasu masu lalurar zaben abinci a can zaman su na Makka.
Kazalika, daga cikin shawarwarin da wannan kwamiti ya bayar har da batun gyaran ofishin ita kanta hukumar domin tabbatar da samun kyakkyawan yanayi a lokacin gudanar da fara aikin. Daga cikin gyaran har da batun rage duhuwar itatuwa da ciyawun da suke cikin harabar hukumar, fitar da fili na musamman ga masu sayar da abinci da sauran kayan sayarwa a wajen hukumar maimakon cunkushewa da ake yi tare da maniyatan. Hatta da masu zuwa bankwana ko tariyar alhazan za'a kebe masu wuraren ajiye ababen hawansu a wajen harabar maimakon cunkushe filin da ma'aikata ke ajiye nasu. Kazalika, za'a lura da masu zirga-zirga aciki da wajen harabar hukumar. Su kan su masu canjin kudi za'a fitar masu da wuraren da zasu gudanar da harkokin su.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Dankama yace, bada jimawa ba za'a fara bayar da bita ga maniyatan, inda Daraktan ya shawarci maniyatan da su gwamatsi malamai domin karin samun ilmin yadda ake yin aikin domin samun yin aikin Hajji Mabrur. 

Post a Comment

Previous Post Next Post