GWAMNA RADDA YA KAI ZIYARAR TA'AZIYA A GARIN 'YANNASARAWA WANDA 'YANBINDIGA SUKA KAI MA HARI A MAKON DA YA GABATA

GWAMNA RADDA YA KAI ZIYARAR TA'AZIYA A GARIN 'YANNASARAWA WANDA 'YANBINDIGA SUKA KAI MA HARI A MAKON DA YA GABATA.

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

          Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda ya kai ziyarar ta'aziya da jaje ga al'ummar 'Yannasarawar Faskari dake karamar hukumar Faskari wanda 'yanbindiga suka hari har suka halaka mutum Takwas a garin tare da raunata wasu a ranar Litinin din da ta gabata,19 ga Fabrairu, 2024
     Dakta Radda wanda Sakataren Gwamnatin jiha, Barista Abdullahi Garba Faskari ya wakilta ya nuna alhininsa akan bayin Allah da suka rasa rayukansu, tare da jajanta ma wadanda aka raunata da kuma rokon Allah Ya kubutar da mutanen da 'yanbindigar suka tafi da su.
Kamar yadda wata snarwar manema labarai ta fito daga ofishin Darakta Labarai na ofishin. Sakataren gwamnatin Jahar Alhaji Abdullahi Aliyu' Yar'aduwa ta ce, Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya gafarta masu, ya baiwa iyalansu hakurin jure wannan rashin da aka yi, wadanda aka konewa dukiya kuma, Allah Ya mayar masu da mafi alheri. Ya kuma jaddada matsayin gwamnatinsa na ci gaba da daukar dukkan matakan da suka dace don kawo karshen aiyukan 'yanbindiga a fadin jihar ta Katsina.
     Sanarwar ta kara da cewa, bayan ya zagayawa da Sakataren yayi don gani da ido har ila yau ya mika sakon ta'aziyar Gwamna Dikko Radda a gidajen iyalan wadanda aka kashe. Kazalika, Sakataren Gwamnatin ya kuma duba gidaje da shaguna da moticin da 'yanta'addar suka kone kurmus.
       Wani daga cikin 'yanbangar garin wanda aka fafata da shi, ya ce 'yan ta'addar sun fado garin ne da misalin karfe tara na dare inda suka fara musayar wuta da su amma saboda yawa da kuma muggan makaman da suka zo da su ya sanya 'yan ta'addar suka ci karfin su.
       Har ila yau, Danbangar ya mika wa Sakataren Gwamnatin takardar lissafin ta'adin da aka yi ma garin inda suka kashe mutum 8, aka raunata 13, suka kora mutum 45, (mata 37 da maza 8) wadanda a cewarsa galibin su yara ne 'yan sakandare.
       Sai dai ya ce tunda abin ya afku kwana 6 ke nan ba a ji duriyar wadanda aka sacen ba, saboda har yanzu 'yanbindigar ba su bugo waya ba, don haka suke rokon gwamnati da ta taimaka wajen ganin an kubutar da su.
Haka kuma 'yanbindigar sun kone motocin daukar kaya (kanta) guda biyu, da bus guda 1 da kirar Golf guda 4 sai gidaje 10 da shaguna 12.
  Al'ummar 'Yannasarawar sun yaba ma Gwamna Dikko Radda da wannan ziyarar, sun kuma roki a samar masu da jami'an tsaro kana a gyara masu hanyar mota daya tilo da ta shigo garin da daga Daudawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post