Waiwaye: NURTW A JAHAR KATSINA NASARORI DA KALUBALE DAGA 1988 ZUWA YAU

Waiwaye: NURTW A JAHAR KATSINA NASARORI DA KALUBALE DAGA 1988 ZUWA YAU

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
        Alhaji Musa Garba Yandoma 
An kirkiro jahar Katsina acikin watan Satumba na shekarar 1987 karkashin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida daga tsohuwar jahar Kaduna. 
Acikin shekarar 1988 kungiyar NURTW ta shigo jahar ta Katsina daga reshen kungiyar dake jahar Kaduna. Shugaba na farko da ya zo da kungiyar kuma ya jagorance shi Alhaji Isa Marmara wanda aka bude ofishinta a bisa benen gidan Nasara Club dake Sabon layi. Shi ne shugaba na farko da ya fara samun nasarar tallata kungiyar acikin jahar kasancewarta a matsayin bakuwa. Shugaban duk da wannan nasara da ya samu har ila yau, hakan bai hana ya fuskanci kalubalen rashin iya gudanar da shugabancin kungiyar kamar yadda ya dace, har ya janyo canza shugabanci. Alhaji Abdu Macukule ya dare kujerar mulkin bayan kuma an mayar da ofishin kungiyar a can kusa da babbar tasha. 
Marigayi Macukule bai karasa wa'adin mulkin shi ba ya fuskanci kalubale kamar yadda na baya ya samu. Bayan wani taro da 'yan kungiyar suka yi a Jibia, an sabke shi Macukulen inda Alhaji Yusuf Haruna ya karbi shugabancin kungiyar bayan kafin nan shine Ma'ajin kungiyar. Alhaji Yusuf ya amshi wannan shugabanci a cikin shekarar 1999. Shi ne kuma shugaban kungiyar da yayi shekaru 12 a bisa wannan shugabanci(1999-2011)
Kadan daga cikin irin nasarori da kalubalen da shugabancin Yusuf Haruna ya samu acikin shekaru 12 na shugabancin kungiyar NURTW ta jahar Katsina. 
1. Kokarin hada kan 'yan kungiya 2. Kara bude wasu rassuna 3. Kawo Shugabanni na kasa (lokacin su Gidado Hamma/Shuwa) don yin taro a jahar 4. Samarwa 'yan kungiya bashin motoci da suka biya a hankali 5. Samar da ofishin kungiyar wanda yake mallakin ta ne, wato, Hedkwata. 6. Ba wasu sassa damar cin gashin kai, wato tsakanin masu kananan motoci da bus-bus da tireloli. Tsohon shugaban ya samu nasarori iri-iri acikin wadannan shekaru 12 da yayi bisa gadon mulkin wannan kungiyar. 
KALUBALE - Duk da kasancewar Alhaji Yusuf Haruma shugaban da ya rike wannan kungiyar ta NURTW har na tsawon shekaru 12 kuma shine shugaban da ya kara fiddo da martaba da nasarorin da kungiyar ta samu acikin wa'adin na shi, hakan bai hana shi fuskantar wasu matsaloli manya da kanana ba. Kadan daga cikin su sun hada da fuskantar rabuwar kan 'yan kungiyar bisa zargin rashin adalci da kuma kokarin mayar da kungiyar tamkar ta shi wadda babu mai ikon fadin wani ra'ayin shi ko neman wani shugabanci sai wanda yake so. Irin wannan kalubake shine sanadin samuwar kafa kungiyar NARTO da sauran wasu kungiyoyin da suka rika fitowa a jahar. Har ila yau, wasu daga cikin tarurrukan da shugabannin kasa na kungiyar ke zowa a jahar na da nasaba da wani kalubalen da yake samu musamman akan batun cigaba da jagorancin kungiyar bayan karewar wa'adin da yake a kai. Irin haka ne ta hanyar sa bakin manyan kungiyar daga sama ya jaza har yayi tsawon shekaru 12 yana mulki. Zarge-zarge akan batun mu'amullan kudaden kungiya kuwa ba'a magana. Har ila yau, a wajejen karshen wa'adin shi na shekaru 12 ne aka samu wani kalubalen tsakanin Katsina, Kano da Maradi ta Jamhuriyar Niger. Wannan matsala da farko tayi kamari sosai domin har sai da kai maganganu marassa dadi sun fara shigowa. Amma Allah cikin nashi ikon ya kawo saukin warware ta ta hanyar yin tarurruka da aka a can Maradi, Magamar Jibiya da kuma garin Mai'aduwa. Shugaba Yusuf Haruna ya sabke daga mulki cikin ruwan sanyi harma ya zama shugaban shiyyar arewa maso yamma na kungiyar. 
Bayan ajiye shugabancin Alhaji Yusuf Haruna sai Sajen Haruna Muhammad(marigayi) ya karbi ragamar shugabancin kungiyar a shekarar 2011 har zuwa 2019. Acikin shekaru 8 da yayi a bisa kujerar, Sajen Haruna ya fara gyara ginin hedkwatar inda aka samar da ofishin shugaba, sakatare da ofishin ma'aji sai kuma babban ofishin da za'a iya taron shugabanni, makewayi da sauran wasu kayan ofis. 
Har ila yau, marigayin a lokacin mulkin nashi ya sake nemawa 'ya'yan kungiyar bashin motoci daga gwamnati. Kazalika, lokacin mulkin na shi an Æ™ara samun zaman lafiya a tsakanin juna. Marigayi Sajen Haruna shi ne wanda ya kawo shirin bayar da tallafi ga 'yan kungiyar a lokacin da wata lalura ta samu kamar yadda yake É—aya daga cikin manufofin kowace kungiyar. Shi ma a lokacin mulkin shi shugaban kungiyar na kasa sun sha zowa taro a jahar(Yasin). Duk da haka, marigayin bai wuce fuskantar kalubalen ba, inda ake ganin cewar ya cika yin sanyi-sanyi ko rashin daukar matakin da ya dace. Har'ila yau, wasu sun yi zargin kamar ya fidda wasu daga cikin shugabannin da suke aiki tare tamkar 'yanlele wadanda basu laifi. Ya sha fuskantar korafe-korafe da dama, amma duk da haka, an rabu lafiya inda shi ma ya wuce ya shugabancin shiyyar arewa maso yamma. 
A shekarar 2019 ne aka zabi matashi a matsayin shugaban kungiyar. A tarihin zowar kungiyar a jahar Katsina, Alhaji Musa Garba 'Yandoma shi ne matashin da ya fara shugabancin kungiyar wanda shi ma ya zo da irin nashi salon mulkin. Daga cikin irin abubuwan cigaban da ya kawo a kungiyar akwai wani babban aiki na sake fasalin hedkwatar kungiyar. A can tana a matsayin mai ofisoshi 3 sai karamin dakin taro. Alhaji Musa 'Yandoma duk da kalubalen da aka shiga na É“ullar cutar korona a 2020 har zuwa 2022,matsalar da ta addabi duniya baki daya musamman ta fuskar karya tattalin arziki, rashin isassar walwala da sauran makamantan haka, wannan bai hana shi yin amfani da basirar da Allah ya bashi ba ta sake fasalin ginin hedkwatar inda ya mayar da ita bene mai hawa guda. Maimakon ofisoshi 3 da ake da su a da, sai ya zamo a saman benen anyi ofisoshi 5,wato,ofishin shugaba, sakatare, babban matakin shugaba, ma'aji da kuma ofis guda na ko ta kwana. A kasan bene anyi sito da babban dakin taro. 
 'Yandoma duk da wancan yunkuri da ya zo da shi na zamanantar da harkokin kungiyar domin ta zamo daidai da lokacin da ake ciki musamman ta inganta harkokin kungiyar, shi ma ya fuskanci matsalolin da za'a ce shi ne wanda Allah ya jarabta da su. Farko dai ya share shekaru uku cikin wani yanayi na game duniya ta fuskar matsalolin tattalin arziki da sauran aiyukan ci gaban al'umma sanadiyar bullar waccan cuta ta korona da kuma batun faduwar darajar naira, babban wani iftila'in da ya same shi tare da wanda ya gada kuma don saboda hidimar kungiyar. Alhaji Musa tare da marigayi Sajen Haruna sun fuskanci iftila'in fadawa hannun 'yan boko haram akan hanyar su ta zuwa hidimar kungiyar wanda wannan hari da aka kaiwa jirgin kasar da suke ciki yayi sanadiyar mutuwar shi Sajen yayin da shi kuma 'Yandoma ya kasance hannun wadannan 'yan boko haram har na tsawon watanni 7. Kenan kusan ace' Yandoma ya kwashe tsawon mulkin shi na shekaru 4 cikin mawuyacin hali da kalubalen da babu wani shugaban da ya rike wannan kungiyar acikin irin halin da ya shiga. 
Lokacin da ya kamata ace ya cigaba da aiwatar da aiyukan kungiyar bayan Allah ya kubutar da shi daga hannun miyagu, sai kuma batun rufe wasu manyan tashoshi 5 na cikin garin Katsina ya ta so. Ba tare da hayaniya ba, wato, a sirrance, bayanai sunce yayi ta kai gwabro da mari na ganin cewa ba'a raba jama'ar shi da wajen samun abincin su. Allah cikin ikon shi yasa hakar shi ta cimma ruwa in banda tasha guda, wato, tashar Kofar Durbi inda gwamnati tace, al'ummar unguwar suka nemi a tayar da ita don a maye gurbin da makaranta. 
Har ila yau, batun zabe ya shigo a wannan lokaci domin wa'adin mulkin shi na shekaru 4 ya cika. Saidai Musa 'Yandoma ya sake hayewa bisa shugabancin kungiyar a karo na biyu bayan wata yarjejeniya da aka yi da masu ruwa da tsaki na kungiyar akan bashi damar yin wannan wa'adi na biyu. Waccan yarjejeniya tayi matukar tasiri akan wani kalubalen da wannan zabe ta taso. Amma Allah cikin ikonsa ya kawo karshen tirka-tirkar da ta shigo. An sake rantsar da Alhaji Musa a karo na biyu a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2023 ba tare da samun wata hatsaniya ba kamar yadda ake gani wasu yankunan kungiyar a wasu jihohin suke yi. 
Alhaji 'Yandoma ya sake hawa kujerar a karo na biyu har ila yau, a bisa halin matsi da kasar take ciki. Wannan hali na matsin bai sa shugaban ya shiga cikin wata fargaba. Hasalima, a kara kira yayi ga membobin kungiyar NURTW a ranar da aka rantsar da shi cewar, su zo a hada karfi da karfe don kawo cigaban kungiyar domin ita ce kungiyar da suka sani kuma suke takama da ita. Duk mai son cigaban kungiyar indai da gaske yake yi, to, yanzu ne da zai fito ya bayar da tashi gudunmuwar. 

Post a Comment

Previous Post Next Post