KUDIN AIKIN HAJJ NA 2024 KOWACE JAHA TA DEBO DA ZAFI BAKIN TA - NAHCON
Daga Muhammad Ahmad Musa
Da Kabir Ahmed S/Kuka
Kamar yadda wasu bayanan da suka fito daga ofishin Mataimakiyar Darakta sashen hulda da jama'a na hukumar kula da aiyukan Hajji ta Æ™asa NAHCON Hajiya Fatima Usara ta shaida cewar Shugaban hukumar na riko Malam Jalal Ahmad Arabi ya cigaba da ganawa da Ma’aikatansa da Jami’an hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohi da Kuma kamfanonin dake jigilar Aikin Hajjin don bayyana musu irin muhimman batutuwan da ya kalato yayin ganawarsa da Ministan Harkokin Wajen Saudiya bayan kammala taron sa hannu bisa yarjejeniyar fahimta da aka yi acan kasa mai tsarki akan shirye-shiryen aikin Hajji na 2024 mai zuwa
Malam Jalal Arabi ya janyo hankullan dukkan bangarorin zuwa Karancin lokaci da ake da shi akan haka ya nemi jami'an da su kara jan damarar fuskantar shirye-shiryen aiwatar da tsare-tsaren Aikin Hajjin na 2024 wanda zasu kasance kamar haka :-
a) Idan Najeriya na son kasancewa kusa da guraren jifan shedan (Jamrat) to fa dole Jihohi su gaggauta biyan duk kudaden da Alhazai suka ajiye a gurin su zuwa NAHCON don ita kuma ta biya hidimomin da za ayi wa Alhazai a Muna da Arafat yayin Aikin Hajjin na bana.
b) Cunkoson Muna da cewa kalubale ne da ita kanta Saudiyya na neman hanyoyin magancewa.
c) Dukkan Shuwagabannin jin dadin alhazai na jihohi na da damar daddale kudaden duk hidimomin da za su fi dacewa da Alhazansu kai tsaye da dillalan da suke bayar da hidimomin(Agents)
Shugaba Jalal Arabi ya shaidawa taron cewa aikin Hajjin wannan shekarar na iya ruwa fidda kai ne don farashin Hajji ba zai zama bai daya ba ga jihohin kasar. Dacewar kowacce Jiha ta daddale farashin masaukai da ciyarwa mafi arha ga maniyatan ta wanda ta haka farashin kujerar wannan jihar zai yi sauki.
d) pJihohi ne za su tsara nau’ukan abincin da za su gabatarwa masu yi musu girki don daddale farashin su.
e) Malam Jalal Arabi ya gargadi Ma’aikatansa da lallai kada a kaucewa ka’idojin da aka gindaya na tabbatar da Alhazai sun mori kudadensu akan kowacce hidimar da suka biya.
Har'ila yau, Shugaban NAHCON yayi tsokaci ga Kamfanoni Masu Zaman Kansu:
1- Ya jinjina musu da hadin kan da suke bayarwa a wajen aiyukansu. Ya kuma shawarce su su kattaba duk wata yarjeniyoyinsu a rubuce.
2- Su tabbatar da sun samarwa Alhazansu masu hidima nagari don dadadawa Mahajjata sosai.
3- Ma’aikatan NAHCON kuwa yace su ninka azamarsu, suyi aiki da ka’idojin da aka sake ingantasu.
Sanarwar ta ce, Shugaba Jalal zai cigaba da ganawa da sauran abokan aikin Hajjin dake Saudiyya da suka shafi ziyarar kamfanonin sufurin sama da na motocin daukar Mahajjata a Makkah da Madinah don daddalewa da kididdige kudin Hajjin baban. NAHCON Za ta cigaba da bibiyar komai don samun alkalumma marassa shubuha.