"KU BAYYANA KADDARORIN KU" GWAMNA RADDA GA JAMI'AI DA MA'AIKATAN GWAMNATIN JAHAR KATSINA

"KU BAYYANA KADDARORIN KU" GWAMNA RADDA GA JAMI'AI DA MA'AIKATAN GWAMNATIN JAHAR KATSINA  

 Daga Kabir Ahmed S/Kuka
 A wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, Malam Dikko Umaru Radda PhD, ta bayyana cewa, Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayar da tabbacin cewa duk masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati a jihar za a karfafa masu guiwa wajen bayyana kadarorin su,yana mai jaddada cewa irin wannan nuna gaskiya yana da mahimmanci.
 Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin Barista Murtala Aliyu Kankia, mukaddashin shugaban hukumar da’ar ma’aikata ta CCB a gidan gwamnati Katsina.
 Yayin da yake karbar bakuncin shugaban hukumar ta CCB, Gwamna Radda ya jaddada kudirinsa na samar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikatan jaha ta Katsina.
 A cewarsa, akwai bukatar jami’an gwamnati su fara bayyana kadarorin su ga hukumar CCB, idan har suna da sha’awar yin aikin gwamnati.
 A cikin jawabinsa, Barr. Aliyu Kankia ya bayyana rawar da Ofishin su ke takawa ba wai kula da bayanan kadarorin ne kawai ba, har ma da tabbatar da bin ka’idojin da’a na jami’an gwamnati.
 “Wannan ya hada da magance batutuwan da suka hada da cin hanci da rashawa, hana yin aiki a kasashen waje, zama mamba a kungiyoyi na musamman, gudanar da asusun ajiyar banki na kasashen waje, da takaita ayyukan kasuwanci da noma,” in ji shi.
 Kankia ya yi gargadin cewa jami’an da ke boye kadarori ba tare da tantance kaddarorin da suka dace ba za su ba wa gwamnatin tarayyar Najeriya su muddin aka gano haka. 
 Ya kuma zayyana hukuncin da za a yanke wa duk wanda ya yi karya, ciki har da dakatar da rike mukaman siyasa na tsawon shekaru goma ko kuma barin mukamin a yanzu.
 Da yake amincewa da fara gudanar da atisayen tantancewa wanda ya kunshi manyan masu rike da mukaman siyasa, sakatarorin dindindin, da shugabannin hukumomin gwamnati, Mukaddashin Shugaban CCB ya nemi goyon bayan Gwamna Radda wajen karfafa bayyana kadarorin da aka samu.
 Ya kuma nemi goyon baya daga sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da aikin ofishinsu yadda ya kamata.

Post a Comment

Previous Post Next Post