Hajj 2024: MATASHIYA GA MANIYATAN JAHAR KATSINA AKAN ZUBA KUDIN AJIYA KAFIN LOKACIN YA ƘARE

Hajj 2024: MATASHIYA GA MANIYATAN JAHAR KATSINA AKAN ZUBA KUDIN AJIYA KAFIN LOKACIN YA ƘARE

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
          
Hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina ta sake yin kira ga maniyatan Jahar musamman waɗanda suka fara ajiye kuɗin da basu kai naira milyan huɗu da rabi (N4.5milyan) ba domin biyan kuɗin aikin Hajjin 2024 da suyi hanzarin cikawa kafin wa'adin da aka bada wanda bai wuce 'yan kwanaki ya ƙare domin bayar da damar ci gaba da sauran shirye-shiryen tafiyar da aiki kamar yadda ƙasar Saudiya da kuma hukumar dake kula da Aikin Hajji ta kasa NAHCON suka ajiye.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama yayi wannan kira tare da tunasarwar. Babban Daraktan har ila yau, yayi kira ga sauran maniyatan dake son zuba kudin nasu da suyi hanzarin yin hakan domin samun damar sabke wannan farali. Alhaji Yunusa ya ƙara da cewa shirye-shiryen aikin Hajjin na 2024 ya sha bamban da na shekarun baya kamar yadda hukumomi a ƙasar ta Saudiya suka sanar. "In ba'a manta ba, hukumomin Saudiyya sunce zasu rufe bayar da biza ga maniyata kwana 50 kafin ranar Arfa, abin da ya zamo tamkar baƙo idan aka kwatanta da shekarun baya wanda har kwanaki kaɗan kafin ranar ana samun bizar".
Alhaji Yunusa ya ƙara da cewa, samun ƙarin wata guda da aka yi daga lokacin da aka fara bayarwa na watan Disamba zuwa ƙarshen wannan wata na Janairu ba ƙaramar dama ba ce, wadda kuma yake da yaƙinin cewar maniyatan Jahar Katsina ba zasu bari a bar su a baya ba domin sun saba zama a sahu na gaba-gaba a wannan aikin ibada a shekaru masu yawa. "Har yanzu ƙofa a buɗe take ga masu niyya acikin waɗannan 'yan kwanaki. Sannan muna ƙara shaidawa maniyata cewar, hukumar mu ita ma ta shirya tsaf domin ganin cewa ta ci gaba da riƙe kambinta na kyautatawa maniyatan tun daga nan gida har zuwa ƙasa mai tsarki. Akan haka ne ma shi Mai girma Gwamna Malam Umar Dikko Radda ya sha alwashin ci gaba da ba wannan hukuma duk wani abinda ta nema yake bata. Muna godiya matuƙa akan wannan".
Sai dai Babban Daraktan ya ja hankalin maniyatan da su guji sauraren jita-jitar da wasu ke yaɗawa a tsakanin al'umma musamman akan batun kuɗin ajiyar naira milyan huɗu da rabi da wasu ke cewa wai kuɗin aikin Hajjin bana na iya haura milyan biyar. Daraktan yace, jama'a su ji tsoron Allah su sani aiki ne na ibada suke tsoratar da wasu maniyatan akan ƙin yi. Yace, in ba daga bakin hukumomin da abin ya shafa aka ji labari, a bar yaɗa abinda ba'a da tabbas. Akan haka yayi kira ga maniyata da sauran jama'a akan cewa, duk wani abinda basu fahimta ba da suje ofishin hukumar mafi kusa da su don neman ƙarin bayani. 

Post a Comment

Previous Post Next Post