Hajj 2024 : ƘARIN WATA DAMA GA MANIYATAN JAHAR KATSINA TA AJIYAR KUDIN SU
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Kamar yadda hukumar kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON ta sanar da ƙarin wa'adin ajiyar kudin aikin Hajji na 2024 na naira milyan hudu da dubu dari biyar (N4.5milyan)har zuwa ƙarshen wannan wata na Janairu akan haka hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina ke ƙara yin kira ga maniyatan dake son sabke farali a wannan shekara da suyi amfani da wannan dama don biyan wadannan kudin ajiya kafin wa'adin ya ƙare.
Kamar yadda hukumar ta sanar daga ofishin Babban Daraktan Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama wadda jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ya shaidawa wakilin mu, tace, wata dama ce da maniyatan suka samu wadda ya kamata su yi amfani da ita a daidai lokacin da ya dace, domin hukumar na da yakinin cewar maniyatan tuni suka jira samun karin wa'adin kasancewar kowa yasan jahar ta manoma ce da kasuwanci.
Kazalika, hukumar ta ƙara jaddada matsayinta na wanda ya riga biya shi za'a fara ba fifiko domin ganin ya samu duk wasu abubuwan da ake bukata cikin sauri da natsuwa.
"Kamar yadda aka sani, bayan amincewar Maigirma Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda, tuni wakilin hukumar suka bi takwarorin su na sauran jihohi zuwa kasar ta Saudiya karkashin jagorancin Kwamishinan harkokin addini Honarabil Ishak Shehu Dabai tare da shugaban hukumar Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai sai Babban Daraktan Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama a inda Ambasadan Najeriya Alhaji Yusuf Maitama Tugga zai jagorancin babbar tawagar karkashin hukumar kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON bisa jagorancin Jalal Arabi domin zaman tattaunawar fahimta da hukumomin na Saudiya sashen dake kula da aiyukan Hajjin da Umra.
Shi dai wannan zama ana sa ran za'ayi bisa batun kama masabkai ga maniyata, harkokin abinci da kuma batun zaman su a Minna da sauran wasu batutuwan da suka hada da harkar sufuri.
Kamar yadda ake sa rai, hukumar jin dadin alhazan ta jahar Katsina zata yi iya kokarin ta na ganin ta samawa maniyatanta da zasu je wannan aiki na 2024 masabkai masu kyau kuma kusa da Harami kamar yadda ake fata. Indai za'a iya tunawa, hukumar har kyaututtuka ta amsa bisa ga kokarin ta na kyautatawa mahajjatanta, kyautatawar da ake sa ran ta wannan shekara zata dara na baya, kamar yadda yake yana daga cikin gudurin shi Maigirma Gwamna Radda na ganin anyi aikin na wannan shekara ba tare da samun kowace irin matsala ba.