YADDA AKA GUDANAR DA BIKIN RANTSAR DA SABBIN SHUGABANIN NURTW NA JAHAR KATSINA

YADDA AKA GUDANAR DA BIKIN RANTSAR DA SABBIN SHUGABANIN NURTW NA JAHAR KATSINA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar alhamis 30 ga Nuwamba, 2023 aka yi bikin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar NURTW ta ƙasa reshen Jahar Katsina a dakin taro na hukumar dake kula da kananan hukumomi a cikin babban birnin Jahar. Kamar yadda tsari da dokokin kungiyar suka tanada, ana yin zaben sabbin shugabanni a duk bayan shekara hudu.
Bikin rantsuwar tare da kaddamar da shugabannin wanda wakilin uwar kungiyar ta kasa Kwamared Sulemain Danzaki ya jagoranta anyi shi cikin nasara. Kamar yadd wasu daga cikin masu jawabai da aka gaiyata musamman Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda da sashen hukumar kiyaye hadurra ta kasa, wakilin jami'an dake kula da motoci(VIO) jami'an hana sha da fataucin miyagun kwwyoyi, jami'an 'yansanda da sauran kungiyoyin da suka hada da na kanikawa da masu haya da babura da sauran masu ruwa da tsaki. Mafi yawan masu jawaban sun jijinawa kungiyar akan irin yadda take bin doka da oda akan tafiyar da harkokin ta. Kazalika, an shawarce su da su bude wani sashe wanda zai kula da batun shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran irin su.
Kafin bayar da wannan rantsuwar kama aiki, sai da shi wakilin uwar kungiyar ta kasa Alhaji Sulemain Danzaki ya shaidawa mambobin kungiyar cewa, ba sun zo ne don tilastawa kowa akan zaben wani ko wasu ba. Har zuwa wannan lokacin babu wanda aka hana shigar da wani korafi akan zaben ba. Amma saboda dukkan 'yan kungiyar sun amince da ci gaba da shugabancin ƙungiya a karo na biyu, babu wanda ya fito ya yi wata magana akai sai ma nuna murna da farin ciki. Wakilin kungiyar kwadago ta jahar ya gabatar da rantsuwar.
Tun farko kafin zuwa ga yin zaben, sai da Maigirma Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar sufuri(KTSTA) Alhaji Haruna Musa Rigoji ya wakilta ya ja hankalin mambobin akan cewa, kada su manta da irin nauyin dake kan su na daukar nauyin rayuka, kaya da kuma ita kanta motar wanda dukkan su alhakin tafiyar su da shi kan shi direban duk sun rataya ne akan shi. Wakilin Gwamnan har ila yau, yayi alkawalin isar da sakon yan kungiyar na sayo masu motocin da zasu rika biya a hankali.
A naji jawabin, shugaban kungiyar na jaha wanda aka rantsas a karo na biyu Alhaji Musa Garba Yandoma yayi godiya mambobin kungiyar akan irin hadin kai da goyon bayan da suke bashi da kuma wanda yace yana da yakinin zasu ci gaba da ba shi fiye ma da na baya. Sannan yayi kira gare su da su cigaba da bin dokokin kasa, dokokin hanya da kuma dokokin tuki. Sannan ya kara jan hankalin su akan cigaba da aiyukan jin ƙai da aka san 'ya'yan kungiyar na bayarwa ga mabukata. Kazslika, su ci gaba da tsare hakkin fasinja da na masu motocin da suka danka amanar su gare su. "Mu sani, duk abin da muka yi walau na alheri ko akasin haka, to akwai ranar da zamu yi bayani mu da kanmu ba wani ba".
Shugaban bayan ya jinjinawa gwamnatin jahar ta Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda akan irin yadda take kokarin kawo karshen matsalar tsaro dake addabar jahar, ya kuma yabawa Gwamna akan irin abubuwan da yake yi na tallafawa talakawan Jahar ba tare da nuna wani bambancin siyasa ba. Alhaji Musa ya kawo misali da irin yadda Gwamnan da kan shibya rika bayar da kayan tallafin da gwamnati ta rika baiwa mabukata da masu karamin karfi. Yace wannan ba karamin al'amari ba ne. "Kazalika, muna kara mika godiyar mu ga Maigirma Gwamna bisa ga irin yadda ya dakile batun tayar da mu daga cikin tashoshin da muka dade muna neman abinci acikin su. Gaskiya wannan ba karamin aiki ba ne tare da taimakawa al'umma domin Allah ne kadai yasan wadanda ke cin abinci a ciki. Anan ina so inyi amfani da wannan dama domin mika kokon barar mu ga Maigirma Gwamna. Kowa dai yasan irin halin da ake ciki a kasar nan. To mu babban tallafin da muke bukata a wajen Maigirma Gwamna shi ne, a saya mana motocin da zamu rika biyan kudin su a hankali domin rage zaman kashe wandon da wasu direbobin ke yi".
Shugaba Alhaji Musa wanda yayi jawabi mai ratsa jiki, a karshe ya tabbatarwa yan kungiyar cewa da ikon Allah duk wasu aiyuka na alheri na ci gaban Æ™ungiya da ya fara a wa'adin mulkin shi na farko, zaiyi iya kokarin shi na ganin ya dora daga inda ya tsaya domin cin gajiyar abin. 

Post a Comment

Previous Post Next Post