SHUGABAN MULKIN SOJA NA NIGER YA BA DAN JAHAR KATSINA LAMBAR AMBASADAN ZAMAN LAFIYA
..... Gwamna RADDA ya cancanci yabo - Muhamad Roja
Daga Kabir Ahmed S/Kuka a Niamey
A tsakiyar wannan satin ne Shugaban kasa na mulkin soja a Jamhuriyar Niger ya mikawa wani matashi É—an asalin Jahar Katsina dake Tarayyar Nigeria takardar shedan zama Ambasadan zaman lafiya. Bikin bayar da takardar shedar wanda aka ba Muhammad Abubakar Haruna da aka fi sani da sunan Roja anyi shi ne bayan amincewar shugaban kasar na mulkin soja wanda Ambasadan zaman lafiya na kasashen Afirka ta Yamma Monsieur Abdallah Ibrahim Sarkin yakin Abzinawan Damagaram ya sanya takardar shaidar hannu kuma ya tamkawa Roja. Birgediya Janar Abdoulrahamane Tiani ya ce, "baiwa Roja wannan matsayi ya zama wajibi duba da irin yadda yake fadi-tashin ganin an cigaba da samun zaman lafiya a tsakanin al'ummar kasashen Nigeria da Niger ta fuskoki daban-dabam musamman a wannan lokaci da kasar ta Niger ke cikin wani hali na matsi da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa kasar" Shugaba Tiani ya ci gaba da cewa, rashin fahimtar da ta nemi kunno kai a tsakanin kasashen biyu in baccin addu'a da kuma sanya bakin wadansu manyan mutane tare da kokarin wayar da kan al'umma akan matsayin al'ummar Nigeria musamman daga arewacin kasar da kuma matsayin ita kungiyar da har yanzu ba'a san inda lamarin ya tsaya ba.
"Mun sani makiya ci gaban kasar mu ne suka shirya duk wani makirci don ganin sun hada mu fada da 'yan uwanmu ta yadda zasu samu damar ci gaba da kwashe mana dukiyar kasa, abin da muka gano kuma in Allah ya so ba zasu yi nasara ba. Niger kasa ce mai 'yancin kai da cin gashin kanta, ba zamu kara bari ana kwashe mana arzikin kasa ba ana mayar da mu bayi. Wannan gwamnati ta sha alwashin kawo karshen zaluncin da ake yi mana. Zamu ci gaba da hada kanmu baki dayan 'yan kasa domin ciyar da kasar mu gaba, ba zamu da mu da duk wani kunci ko barazanar wata kasa don karya mana kwarin guiwa ba. Tabbas muna sane kuma mun tabbata al'ummar Nigeria 'yan uwan mu suna nan tare da mu, suna goyon bayan mu kuma suna yi mana addu'a. Muna godiya".
Shugaban mulkin soja na Niger Bridg. Janar A. Tiani, Roja da wasu mahalarta taron a fadar shugaban kasa
Da ya juya akan taron da shi wannan matashi ya tara domin wayar da kai da kuma kokarin ganin an kara samun hadin kai a tsakanin juna, Shugaba Tiani ya jinjinawa wannan kokari wanda ya ce, shi ne abu na farko da ya faru a mulkin su na ganin ba wai hadan kan al'ummar kasashen biyu ba, hatta da su 'yan kasar ta Niger wannan taro ya kara hada kansu da kuma kara fahimtar irin zumunci da 'yan uwantakar dake tsakanin mu da Nigeria.
Malam Roja kasa tana yi maka godiya da wannan hidima da kayi. Mun san kai mai son zaman lafiya da son ci gaban kasashen mu ne. Ku ma sauran wadanda kuka baro aiyukan ku da kasar ku kuka zo don gabatar da wannan taro mun jinjina maku. Muna fata ku koma gidajen ku lafiya", inji shugaban mulkin soja na Niger Birgediya Janar Tiani.
Shi ma Ambasadan zaman lafiya na kasashen Afirkan Monsieur Abdallah wanda ya kai gwabro da mari wajen ganin Muhamad Roja ya samu wannan matsayi yace, zama Ambasadan zaman lafiya ba karamin aiki ne ba kuma aikina na zarumai masu kokari da son zaman lafiya. Saboda haka, ya shawarci Roja da ya rike wannan matsayi da muhimmanci bisa gaskiya da rikon amana.
A nashi sashen, Muhammad Abubakar Haruna wanda yake dan asalin karamar hukumar Safana ne ta Jahar Katsina dake Nigeria ne, ya fara da baiyana yadda ya samu kan shi hatta da zaman shi ko ma'amullar shi a ita kasar ta Niger. "Ni mai sana'ar fina-finan Hausa ne tun ma ana nunawa a gidajen sinima. Ina daga cikin farkon mutanen da suka fara kawo 'yan wasan Hausa na Nigeria zuwa nan Niamey. Ina cikin wadanda suka kafa kungiyar yan wasan Kainuwa anan Niamey. Har ila yau, na zagaya manyan garuruwa da wasu jihohin na Niger duk akan batun harkar wasannin Hausa don fadakarwa. Hakan ne ma dalilin zamana anan garin Niamey".
Muhammad Roja ya kara da cewa, "wannan matsala ta juyin mulkin soja anan Niger wadda ta haddasa kungiyar ECOWAS ta kakaba mata takunkumi da kuma yunkurin da kungiyar da farko ta fara fadi na cewar za'a kawo mata harin soja in bata mayar da mulki ga farar hula ba musammam ga shi shugaba Bazoun da suka yiwa juyin ta kawo rudani mai yawa. Babbar matsalar da aka samu, ko ince rashin fahimta da 'yan kasar ta Niger suka samu inda suka yi zaton wai Nigeria ce zata kawo masu hari domin ita ce ke shugabancin kungiyar ta ECOWAS. Matsalar da farko ta fara yin tasiri har ma kiyayya ta nemi ta shigo a tsakani. Wannan kuwa ba karamin abu ba ne. To sai na tsaya nayi tunani cewa, in dai har muna shirya fina-finai ne don fadakarwa da isar da sako ga jama'a, to wannan matsalar ita ce abin da ya kamata mu fadakar da al'umma akai. Mu sani uwa daya uba daya muke a tsakani. Wannan shine babban dalilin da yasa na shirya wannan taron gangami don fadakar da juna muhimmancin zaman lafiya. Na gaiyato 'yan wasa daga Nigeria da wasu masu ruwa da tsaki akan harkar wayar da kan jama'a muhimmancin zaman lafiya tare da ku 'yan jaridu na kasashen biyu, inda muka gudanar da wasanni iri-iri har na tsawon sati guda domin kara dankon zumunci da kuma kokarin warware waccan matsala ta rashin fahimtar matsayin Nigeria na shugabanci da kuma kara sanar da duniya dalilan juyin mulkin da sojojin suka yi da kuma halin da ake ciki a yanzu".
Roja wanda yace, duk rayuwar shi Allah yasa mutun ne shi mai son zaman lafiya. Ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu akan wannan taro domin jama'a sun amfana da shi an kuma kara samun hadewa ta yadda makiran kasashen da suka so su raba mu su haddasa yaki a tsakanin mu don biyan bukatar su haƙar su bata cin ma ruwa ba,kamar yadda ya ce.
Da ya juya akan batun jahar Katsina inda ya fito, Muhammad Abubakar ya ce, "gaskiya Gwamna Malam Umar Dikko Radda ya cancaci yabo da jinjina.
A matsayina na dan asalin karamar hukumar Safana daya daga cikin kananan hukumomin da suke fuskantar matsalar tsaron nan, wallahi babu abinda zance sai yi mashi addu'a. Allah ya bashi duk wani abinda yake nema. Gaskiya wannan mutun ya zamo zakaran gwajin dafi a tsakanin shugabannin arewa ba wai jahar Katsina ba. Duk wani mai son ci gaba da kishin al'ummar shi, to Gwamna Radda ya fito fili ya nuna ya shiga gaban su. Ga irin rahotannin da muke samu, wadannan jami'an tsaro da ya kirkiro ba karamar hikima da baiwa ba ce Allah ya ba shi. Gaskiya, wannan shiri da yayi na kawo karshen aiyukan ta'addanci a jahar da samun zaman lafiya, ya kara mani kwarin guiwa a wajen hada wannan taron zaman lafiyar.
"Ina so inyi amfani da wannan dama inyi kira ga al'ummar jahar Katsina da su baiwa Gwamna Radda goyon baya akan duk wani aikin da ya shirya aiwatarwa. A ajiye batun siyasa waje guda. Jahar Katsina ta samu jagora na gari, mai kishin al'ummar shi mai son ganin suna zaune lafiya".
Masha Allah ♥️
ReplyDeleteWane nan abin farine chiki ne garemu Al umar katsina da Nigeria baki Daya .
Allah yaja zamanin kasar Niger da Nigeria