SAKON TAYA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR KA

SAKON TAYA MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR KA
A madadin kungiyar wasan Kwallon dawaki ta jihar katsina watau "Katsina Polo Club" 

Tana farin cikin taya tsohon shugaban kasar Nijeriya, Janar(mai ritaya) Muhamad Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar shi inda ya cika shekaru 81 da haihuwa a wannan rana ta 17 ga watan Disamba, 2023. Hakika, a cikin shekaru 81 da uba, jigo a wannan kasa tamu ta Nijeriya ya yi a raye a lokacin mulkinsa, al'ummar Nijeriya sun amfana da aiyyukan raya kasa, a lokacin mulkin da tsohon shugaban kasar Baba Buhari ya yi, a karo na farko da karo na biyu, duk da cewa kasar Nijeriya ta shiga wani mawuyacin halin matsin tattalin arziki.
Hakika wannan kungiya na 'kara nuna godiyar ta ga Allah (S.W.T) tare da addu'ar Allah ya kara yima  Baba Buhari jagora a cikin sauran kwanakin da suka rage mashi, Allah ya sanya albarka a ciki.
Wannan sako ne daga shugaban kungiyar na kasa rashen Jihar Katsina Alh. Muhammadu Usman Sarki.

Post a Comment

Previous Post Next Post