Saboda ƙwazo : AN KARRAMA GWAMNA RADDA DA KYAUTAR ƘUR'ANI
Wata cibiyar adana kayan tarihin addinin musulunci tare da tarihin addinin(ICICE) hadin guiwa da ƙungiyar hada kan musulmi ta duniya(OIC) sun karrama Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda ta hanyar ba shi kyautar Al'Ƙur'ani mai dauke da dogon tarihi dake ajiye karkashin kulawar su.
Kamar yadda suka ce, sun ba Gwamna Radda wannan kyauta ne bisa lura da suka yi da shi akan kawo cigaba da yake yi domin inganta rayuwar al'ummar shi musamman akan abin da ya shafi batun tsaro da kuma batun harkar addinin musulunci ba tare da nuna bambancin akida ko na siyasa ba.
Daya daga cikin wadanda suka raka Gwamnan a wajen karbar wannan kyautar wannan karamawa wanda kuma shi ne Sarkin Alhazan Katsina kuma shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Kabir Bature ya shaidawa wakilin ta wayar salula da ya tuntube shi cewar baiyi mamakin wannan bincike na ita wannan cibiya ba. "Ina so ka sani cewar, Gwamna Radda duk irin abin da za'a ce ya aiwatar na alheri da kuma kawo al'ummar sa cigaba acikin dan lokacin da ya dauka da hawansa bisa kujerar jagorancin Jahar kada kayi mamaki.
A matsayina na Sarkin Alhazan Katsina wanda zance na gada, kazalika, wanda ya azawa jagorancin ita hukumar ta alhazan, bakin iya sani na ban taba ji ko a labari ba cewar ga wani Gwamna wanda ya je kasar Saudiya domin bincike da kuma zabarwa jama'ar shi masabki da wadanda zasu yi masu abinci a lokacin da zasu je aikin Hajji sai shi Gwamna Raddan. Ni ganau ne ba wai labari ba domin tare da ni da Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Dankama muka zagaya a garin Makka har ya samu masabkin da yaga yayi mashi kuma kusa da Harami. Banda wannan, dawo yanzu ka duba irin yadda yake yiwa addinin hidima acikin Jahar wanda ba sai nayi dogon bayani ba, al'umma shaida ne", inji Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai