NUJ TA SAMI SABBIN SHUGABANNI A GIDAN TALBAJIN NA JAHAR KATSINA

NUJ TA SAMI SABBIN SHUGABANNI A GIDAN TALBAJIN NA JAHAR KATSINA 
An rantsar da sabbin shugabannin Æ™ungiyar 'yan jaridu reshen gidan Talbijin na jahar Katsina a ranar Alhamis 28 ga watan Disamba 2023. Sabbin shugabannin sun sake hawa bisa kujerun su ba tare da hamayya ba. 
Shugabannin da aka rantsar sun hada da, Aminu Garba Dandagoro a matsayin shugaba, Ahmed Mukhtar Yantaba Mataimaki, Yasir Abubakar Sakatare, Mustafa Dahiru Mani Mataimakin Sakatare. Sauran sun hada da Abdul Aziz Salisu Sakataren kudi sai Sufuyanu Musa mai bincike tare da Shamsu Habibu a matsayin Ma'aji.
Da yake rantsar da su, shugaban kungiyar ta NUJ reshen jahar Katsina Alhaji Tukur Hassan Dan-Ali ya ja hankalin su da su ji tsoron Allah sannan su aiwatar da aikin su bisa adalci ba tare da nuna son kai ba.
Alhaji Tukur Dan-Ali ya ce, shi kan shi ya fara takara tun daga gidan rediyon jahar har zuwa yau duk ana zaben shi ba tare da hamayya ba. Yace, sun yi kokarin yi shi ne, samar da mota ga kungiya da samun wasu filaye tare da inganta hedkwatar kungiya ta hanyar yi mata wasu aiyuka. Yace, zama shugaba ba karamin aiki ba ne musamman a sashen da suke ciki. Zama tamkar almajirai ga kungiyar, yace, wannan wani abu ne da ya zama tamkar ruwan dare ga kungiyar a ma kasa baki daya. Dole ne sai kungiya ta nemi gudunmuwa daga wasu wuraren domin tafiyar da kungiyar. Ya kawo misalai da dama a wasu jihohin da kuma irin yadda suka samu kan su. 
Shi kuwa shugaban kungiyar wakillan sauran kafafen jaridu dake jahar, Alhaji Abdul Hamid Sabo, jan hankali yayi akan yadda 'yan jaridu a jahar Katsina suka samu kansu a yanzu tamkar almajirai. Sabo wanda ya nuna faruwar hakan akan tafiyar hawainiyar da uwar kungiyar ta jaha ke yi akan aikin ta. Sabo ya tuno cewar a nasu sashen cikin yunkurin da suka, har kudi suka tara sama da naira milyan 50 ta hanyar rubuta wasu littattafai biyu da suka yi. A cewar shi wannan ya basu damar maimakon ajiye kudin sai suka yanke shawarar sayen motocin da za'a rika yin haya da su a hukumar sufuri KTSTA wanda sune na farko da suka fara kai motar haya a wannan hukuma.
Akan haka shugaban yayi kira ga uwar kungiyar da sauran rassan kungiyar da cewa, kada su bari waccan daliba mai kama da ta almajirai ta ci gaba. Su dage a wajen aiwatar da aikin su bisa gaskiya ba tare da cin tsoro ba wanda hakan zai kara dago martabar su da aikin na jarida.
Shi ma a nashi dan gajeren bayanin, Alhaji Aminu Musa Bukar wanda yake shugaban kungiya ne na gidan rediyon Companion FM dake Katsina, cewa, yayi su ji tsoron Allah sannan su yi shugabanci bisa adalci da rikon amana.  

 

1 Comments

  1. Wanda aka zaba a matsayin sakatare sunansa Yasir ba Nasir ba, take note pls!

    ReplyDelete
Previous Post Next Post