MUTANE 100 ƘUNGIYAR IZALA TA YIWA AIKIN TIYATA KYAUTA A DAURA
Daga Hamisu Lawal Daura
Kungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa'ikamatus Sunna JIBWIS, reshen Karamar hukumar Daura, Karkashin Jagorancin Injiniya Abba Mato ta daukin nauyin Talakawa Marassa lafiya guda 100 don ayi ma su aikin Hynia da kuma Hypomae(watau Kari) kyauta a fadin Karamar hukumar ta Daura.
Aikin Tiyatar da Injiniya Abba Mato ya jagoranta, ya ce Kungiyar ta yanke shawarar gudanar da aikin ne domin taimakawa ma su Karamin Karfi da ke yankin. Yace sun sami Kudin yin wannan aiki ne daga ribar da su ka samu a Shagon sayar da Magani da suka bude watau Sunna Chemist da ke Daura. Injiniya Abba Mato Ya bukaci ma su hannu da shuni su taimaka don't ciyar da al'umma gaba.
Shi kuwa Shugaban karamar hukumar Daura Bala Musa ya yabawa Kungiyar ta Izala da wannan taimako da ta yi. Ya tabbatar da cewa ƙaramar hukumar Daura za ta tallafawa Kungiyar wajen gudanar da wannan aikin.
Tun farko, shugaban Likitocin da za su yi wannan aiki, Alh. Ali Maibara ya yi bayani yadda za a tantance mutanen da za a yiwa aikin. Yace aikin mataki-mataki ne, wani idan an gama za a sallami mutum ya tafi gida, yayin da wani sai ya kwanta a Asibiti.
Kaddamar da aikin ya sami halartar wakilan Kungiyar Izala na jihar Katsina da na Kasa baki daya ƙarkashin Jami'i mai binciken kudi na Kasa Shiek Bature Dandume