MATASA A RUNGUMI SANA'A DA KASUWANCI - Wazirin Jibiya

MATASA A RUNGUMI SANA'A DA KASUWANCI - Wazirin Jibiya

Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Anyi kira ga matasa musamman na karamar hukumar Jibiya da sun runguri sana'a musamman ta hannu ko kasuwanci domin dogaro da kan su maimakon yawon kashe wando. Alhaji Hamza Sale Wazirin Jibiya yayi wannan kira a lokacin da yake zantawa da wakilin mu. Wazirin wanda ya tunasar da matasan cewa, "an san mu mutanen Jibiya mutane ne masu kokarin yin kasuwanci da sana'o'in hannu wanda hakan ya sa muka sha bamban da wasu wuraren. Kasancewar mu a tarihi masu wannan kwazo ne yasa a lokuttan baya in anga mai yawo kwararo-kwararo to da abincika zata taras baƙo ne, shi ba za'a dauki dogon lokaci ba zai bi sahu".
Alhaji Hamza ya kara da cewa, duk wata baiwa ta albarkatun da Allah ke bayarwa ya ba Jahar Katsina ya kuma ba karamar hukumar ta Jibiya. "Kaga yanzu banda batun noman damina da za'a ce tun na da ne, shi kan shi noman ranin ba'a barmu a baya ba. Duk da matsalar ruwa da muke fuskanta hakan bai hana mu yin noman ba. Muna noma, kayan lambu, kai har da masara da shinkafa da dankali na gida da na turawa. Muna noma rake da duk wani nau'in kayan abinci. Batun sana'a kuwa sata ce kawai bamu yi don bamu gaje ba". Sai dai Basaraken ya nuna takaicin shi ga yadda wasu matasan ke jefa kansu cikin matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda yace suke jefa matasan cikin miyagun aiyukan laifi har a kai ga shiga ta'addanci. "Shin dole ne sai matashi yayi aikin gwamnati don takamar yayi karatu? Mu dubi irin yadda wasu kasashen suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki. Ana tunanin gwamnati ce? Mu yi amfani da ilmin da muka koya don habaka harkokin kasuwancin mu ko sana'o'in mu ta yadda zamu zamanantar su ma na. Amma muna neman mu rika jefa rayuwar mu cikin hadari bayan kuma mune kashin bayan ci gaban al'umma".
Alhaji Hamza ya yaba da irin matakan tsaron da al'ummar Jibiyar ke dauka musamman ta kafa kungiyoyin da suke yi. "Gaskiya a yanzu sai muce muna godewa Allah. Batun tsaro a yanzu sai dai muce za'a yi koyi da jama'ar mu. Baya ga batun tsaro ga aiyukan cigaban da suke kawowa ta hanyar taimakon jama'a. Allah ya saka da alheri. A karshe ya kara yin kira ga gwamnati da ta dubi halin da al'ummar yankin suke ciki don tallafa masu da kuma share masu hawaye akan matsalolin da suke fuskanta na shekara da shekaru. Sannan ya kara yin kira ga al'ummar karamar hukumar da su cigaba da bayar da goyon bayan su domin kawo cigaba har ya zuwa matakin jaha da kasa baki daya musamman akan batun sha'anin tsaro. 

Post a Comment

Previous Post Next Post