KU RIƘE AL'ADAR TSAFTACE MUHALLI DA MUHIMMANCI- Darakta KU KIYAYE YIN BAHAYA A WURI BUƊE - Kanwan Katsina

KU RIƘE AL'ADAR TSAFTACE MUHALLI DA MUHIMMANCI- Darakta
 KU KIYAYE YIN BAHAYA A WURI BUƊE - Kanwan Katsina
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

 Daraktan sashen samar da ruwa da tsaftar muhalli na karamar hukumar Kankara Alhaji Tanimu Ibrahim Bakori ya yi kira ga al’ummar gundumar Ketare da su yi koyi da al’adun tsaftar muhalli. Daraktan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ga Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alhaji Usman Bello Kankara mni a fadar sa.
  A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sarkin Labarun Kanwan Katsina Malam Jamilu Hashimu Gora kuma aka rabawa manema labarai. 
 Sanarwar na cewa, a ranar shida ga wannan wata, jami’an gwamnatin tarayya da na UNICEF za su ziyarci karamar hukumar Kankara, domin tantance matakin da ake bi wajen yin bahaya a fili.
    An ruwaito cewa, Daraktan ya jadadda bukatar al’ummar gundumar Ketare da su kara kaimi wajen kula da tsaftar muhalli domin biyan bukatun da aka gindaya, yayin da ya kuma bayyana cewa, fa’idojin da ke tattare da shirin da suka hada da yin rijiyar burtsatse domin inganta samar da ruwa mai tsafta da gina karin bandakunan yin bahaya a cikin al'umma. Don haka yana neman goyon baya da hadin Kanwan Katsina domin cimma burin da ake so.
 A nasa martanin Kanwan Katsina Alhaji Usman Bello Kankara mni ya tabbatarwa da Daraktan cikakken goyon baya da hadin kai daga magaddai da masu unguwanni domin cimma burin da ake bukata domin al’umma za su ci gajiyar ababen more rayuwa da suka shafi shirin.
 Hakimin ya ce, “a matakin unguwanni da gundumomi tuni aka kafa kwamitoci don tabbatar da nasarar shirin hana yin bahaya a bude”.  Alhaji Usman Bello Kankara ya umurci dukkan masu gungumomi da masu unguwanni da su tabbatar kowane magidanci yana da wurin da ake bukata na bandaki don cin gajiyar aiki tare da bin ka'idar.
 Kazalika, ya umurci dukkan limaman gundumar da su ci gaba da fadakar da mabiyansu a lokutan salloli biyar da sallar Juma’a kan nisantar yin bayan gida a fili tare da lura da cewa tsafta na gaba da tsarki.
 Alhaji Usman Bello Kankara ya yi kira ga al’ummar yankin da su tabbatar sun samu bandakuna a gidajensu sannan kuma su guji yin bahaya a kasuwanni, wuraren ajiye motoci, da makarantu da dai sauransu. Ya yi nuni da cewa zai kai ziyarar bazata zuwa wasu zababbun al’ummomi domin tabbatar da bin ka’ida.

Post a Comment

Previous Post Next Post