Katsina PWB : KU JAJIRCE A AIKIN HAJJ NA 2024 - ED ga ma'aikata ZA MU BA MARAƊA KUNYA - Ma'aikata

Katsina PWB : KU JAJIRCE A AIKIN HAJJ  NA 2024 - ED ga ma'aikata
                          ZA MU BA MARAƊA KUNYA - Ma'aikata

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 

 Sabon Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya tabbatar wa ma’aikatan hukumar cewa zai yi aiki kafada da kafada da mahukunta da sauran ma’aikatan hukumar domin samun nasara.
 Alhaji Yunusa Dankama ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da ma’aikatan hukumar a hedkwatar hukumar dake sansanin alhazai dake Katsina akan shirye-shiryen aikin Hajj na 2024 mai zuwa. 
    Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga ofishin jami'in hulda da jama'a (PRO) na hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ta ce, "Babban Daraktan ya yi kira ga ma’aikatan da su himmatu wajen gudanar da ayyukan da aka dora masu". 
 Ya yi magana sosai a kan bukatar da ake da ita ga shugabanni da ma’aikatan hukumar na su yi hada hannu tare da shi wajen gudanar da aikin da aka ba shi, ya kara da cewa yana nan a cikin hukumar don yin aiki mai kyau da kowane ma’aikaci, ba wai musgunawa kowa ba.  Don haka ya bukace su da su guji lalaci a yayin gudanar da ayyukansu.
 Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya godewa gwamna, Mallam Dikko Umar Radda bisa nada shi babban darakta na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina, inda ya jaddada cewa yana kan wannan aiki domin samun nasara.
  Da yake gabatar da babban daraktan hukumar ga ma’aikatan hukumar, daraktan gudanarwa da samar da kayayyaki na hukumar, Alhaji Sada Salisu Rumah ya bayyana nadin Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama a matsayin babban daraktan kula da jin dadin alhazai na jihar Katsina a matsayin wanda ya dace kuma abin yabawa ne saboda yadda ya tafiyar da aikin.  ya zama shugaban karamar hukuma har sau 5, ya kuma yi dan majalisar dokoki na jaha wanda ya wakilci karamar hukumar Kaita baya ga wasu hidimomin ci gaban al'umma, kazalika, dan siyasa mai mutunci da kuma kishin addini. 
 Alhaji Sada ya tabbatar wa da sabon Daraktan cewa ma’aikatan za su yi duk mai yiwuwa don ganin ya samu nasarar daukaka matsayin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Katsina.
 Sauran wadanda suka yi jawabi yayin taron sun hada da Daraktan ayyuka Alhaji Yusuf Ahmed da Daraktan kudi Alhaji Sagir Abdullahi Inde da na Daraktan bincike da kididdiga Dr Aminu Abdullahi Yammawa. Dukkan su sun bayyana wa Babban Daraktan cewa a shirye suke don gwnin aikin Hajji na 2024 anyi shi cikin nasara. 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post