Katsina PWB : GWAMNA RADDA YA SHA ALWASHIN ƘARA INGANTA AIYUKAN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI - Sarkin Alhazai

Katsina PWB : GWAMNA RADDA YA SHA ALWASHIN ƘARA INGANTA AIYUKAN HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI - Sarkin Alhazai
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Dikko Radda ya baiyana kudurin shi na ƙara inganta aiyukan hukumar jin dadin Alhazai ta jahar domin tabbatar da tafiyar da ita kayar yadda ya dace. Sarkin Alhazan Katsina Alhaji Kabir Bature wanda kuma shi ne shugaban hukumar jin dadin alhazan wanda Gwamnan ya nada bada jimawa ba, ya shaidawa wakilin mu a wata hira da suka a ofishin shi dake harabar hukumar cewa, abu na farko da Gwamnan ya fara yi shi ne, kiran su zuwa ƙasa mai tsarki shi da abokin aikin shi, wato, Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Dankama domin tabbatar da fara samawa maniyatan jahar a aikin Hajji na shekarar 2024 mai zuwa. Sarkin Alhazan wanda yake ɗan-kabar tsaka ne a batun harkokin na aikin Hajjin ya ce, "tun kafin takardar bamu wadannan mukamai su shigo hannun Gwamnan ya kira mu inda muka same a can kasa mai tsarkin domin shi yana can tare da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunibu ba kuma tare da bata wani lokaci ba muka same shi".
"Lokacin da muka same shi ya shaida mani cewar, yana so ya sa hannu shi da kan shi yaga an kyautata mahajjatan jahar. Yace ba zai bar aikin hajji ya lalace ba. Ya ce, lallai matsalolin dake taɓa aikin hajji yana so ya gan su shi da kan shi. Abu na farko da ya fara yi shi ne, bin wuraren da aka sabkar da alhazai har sai da ya samu wanda yaga yayi mashi. Ya kuma baiyanawa masu masabkin irin gyare-gyaren da yake bukata ayi wadanda suka hada da rage cikewar daki domin samun isasshen filin yin walwala ga alhazan a lokacin da suke zaman Makka,kuma masabkan nan kusa da Harami wanda lokacin sallar juma'a har zuwa nan akwai masu bin sallar ta Harami. Haka yayi ga masu abinci".
Sarkin na Alhazai kuma shugaban hukumar jin dadin alhazan ya kara da cewa,Gwamna Malam Umar Dikko Radda yayi haka ne domin tabbatar da cewa ya inganta aiyukan hukumar da kuma aikin na hajji a maniyatan da suka fito daga Jahar ta Katsina. "Tunda nike hidimar aikin Hajji ban taba ji ba wai gani ba cewar koda sakataren gwamnati ba Gwamna ba yaje Saudiyya domin nemawa mahajjatan shi gata a lokacin da zasu je aikin Hajji sai akan Gwamna Radda wanda hakan ya nuna a fili cewar shi mutun ne mai son kawo ci gaba ga al'ummar shi ta kowace fuska.
Sai dai shugaban hukumar ya ce, babban ƙalubalen dake gaban su shine, batun biyan kudin ajiya acikin wani irin yanayi kuma a kurarren lokaci wanda aka ce ana so a biya cikin hanzari. "Mun dai sani cewar babu wani abu da zamu iya canzawa daga cikin aikin, misali, ranar Arfat ko zaman Muna, ko yin jifa da sauran su. Babban kiran mu ga maniyatan shi ne, su fito su biya wadannan kudade kafin lokacin da aka aiyana na ƙarshen wannan wata na Disamba, 2023. Muna dai da kujerun sama da dubu 4 amma har yanzu bamu kai mutun dubu ba, duk kuwa da tasirin da muke da shi a duk lokacin da wannan aiki ya zo. Amma muna fata zamu samu jama'ar kafin lokacin ya kure. Dama da gwamnatin Saudiyya da tamu ana nan ana tattaunawa domin ganin an ƙara sassabta lokacin domin su Saudiyya sun ce zasu rufe bayar da bisa kwana 50 kafin ranar Arfat. Kazalika, muna fata za'a samu ragowar wani abu daga cikin adadin kudin aikin da maniyatan zasu biya. Anan nike so in yi amfani da wannan dama inyi kira ga jama'ar mu masu son sabke wannan farali da suyi hanzarin biyan kafin lokacin ya kure. Mun sani mafi yawan masu zuwa wannan aiki manoma ne da 'yan kasuwar mu, to mun ga irin yadda kakar bana ta kasance, wannan ne ya kara bamu kwarin guiwar cewa, kila ma har sai mun ƙara neman wasu kujerun daga NAHCON domin mun cike wadanda aka bamu.
A ƙarshen, shugaban hukumar ya mika godiyar su ga Gwamna Malam Umar Dikko Radda da ya basu wannan dama ta yiwa addinin musulunci hidima. Ya kara jinjinawa Gwamnan akan irin yadda tayarwa yaki da ta'addanci a Jahar wanda kuma kullum al'umma na yabawa tare da yi mashi addu'a saboda suna gani da kansu ba wai labari ba. Sarkin na Alhazai ya kara yin kira ga al'ummar Jahar da su cigaba da ba Gwamnan goyon baya domin gani ya cika alkawurran da ya dauka da kuma sabke nauyin da Allah ya aza mashi lafiya. 

Post a Comment

Previous Post Next Post