KANWAN KATSINA YA ROKI GWAMNATI DA TA KARA HORAS DA MA'AIKATAN LAFIYA TA YADDA ZASU HORAS DA WASU

KANWAN KATSINA YA ROKI GWAMNATI DA TA KARA HORAS DA MA'AIKATAN LAFIYA TA YADDA ZASU HORAS DA WASU 

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
 Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alhaji Usman Bello Kankara mni ya yabawa Hukumar Inshorar ta NDIC bisa gina dakin haihuwa na zamani a babban asibitin Kankara.
 Hakimin ya yi wannan yabon ne a lokacin kaddamar da sashen dake kula da mata masu juna biyu mai gado 20 wanda hukumar ta NDIC ta gina a matsayin wani bangare na aikin kula da jin dadin jama'a na kamfanoni na CSR.
 Daga nan sai Hakimin na Ketare Alhaji Usman Bello Kankara mni ya yi kira da a horas da jami’an kiwon lafiya domin basu damar horar da wasu, wanda a cewarsa za su ci gaba da ciyar da bangaren lafiya gaba bisa tsarin tafiyar da harkokin gwamnatin jihar a halin yanzu.
 Basaraken ya yabawa gwamnatin Gwamna Dikko Radda bisa yadda ta fara daukar ma’aikatan lafiya a baki dayan jihar tare da ba da shawarar cewa a baiwa ma’aikatan wucin gadi fifiko a cikin aikin.
 Alh.  Usman Bello Kankara mni shawarci kwamitin gudanarwa na asibitin da kwamitin amintattu na asibitin da su yi amfani da tsarin yadda ya kamata tare da kiyaye shi daga lalacewa da barna.
 Kanwan Katsina ya ci gaba da yin kira ga hukumar NDIC da ta mika makamancin irin wannan aikin a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Ketare da ke yankinsa.
 Alhaji Usman Bello Kanwan na Katsina ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran kungiyoyi da daidaikun jama’a da su taimaka wa asibitin da karin gine-gine da kayan aiki domin isar da hidima mai inganci.
 Wadanda suka halarci taron sun hada da wakilin gwamna Dikko Umaru Raddah, kwamishinan lafiya Dr. Bashir Gambo Saulawa, babban manajan gudanarwa na asibitin Dr. Sabi'u Liadi, babban sakataren ma'aikatar lafiya Dr. Ahmed Tijjani Hamza da babban sakataren ma'aikatar Matasa da Wasanni Alh.  Surajo Mika'ilu.
 Sauran sun hada da wakilin NDIC daga ofishin shiyyar Kano, kwamishinan ayyuka na musamman Hon.  Isa Mohammed Musa, da wakilan Abokan Asibiti da sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post