HAJJ 2024: HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA NA DAGA CIKIN WADANDA SUKA YI TARO DA HUKUMAR ALZAHAI TA KASA

HAJJ 2024: HUKUMAR JIN DADIN ALHAZAI TA JAHAR KATSINA NA DAGA CIKIN WADANDA SUKA YI TARO DA HUKUMAR ALZAHAI TA KASA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
    Babban Daraktan PWB A. Y. Dankama
Acikin gaban shirye-shiryen tunkarar aikin Hajji na shekarar 2024 mai zuwa, hukumar alhazai ta Æ™asa NAHCON ta yi wani taro da jagororin hukumomin jin dadin Alhazai na jihohin kasar a marecen juma'ar nan domin tattaunawa da su don ji da kuma sanin matsayar da kowace jaha take ciki dangane da batun shirye-shiryen aikin Hajjin na 2024 musamman akan sanin halin da jihohin suke ciki na samun maniyatan da zasu sabke wannan farali. Taron wanda hukumar NAHCON ta shirya ta hanyar yanar gizo da ake kira, "Visual meeting" Æ™arÆ™ashin jagorancin shugaban hukumar na Æ™asa Alhaji Jalal Ahmed Arabi tare da sauran masu ruwa da tsaki akan aikin Hajjin. 
Kamar yadda ta saba a duk shekara na ganin ta zamo zakaran gwajin dafi ga sauran hukumomin jin dadin alhazai na kasar baki a wajen kokarin ganin maniyatan ta na samun kulawa ta musamman ta fuskoki da dama tun daga gida har zuwa kasa mai tsarki, a wannan karon ma hukumar jin dadin alhazan ta jahar Katsina ba'a bar ta a baya ba wajen ganin ta shiga sahun masu halartar wannan taro kuma ta bayar da irin ta ta gudunmuwar a wajen wannan tattaunawa. 
Kamar yadda wata sanarwar manema labarai da ta fito da ofishin Kakakin hukumar Alhaji Badaru Bello Karofi ta ce, Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Dankama ya jagoranci sauran daraktocin hukumar a wajen zaman wannan taro a ofishin sa dake cikin hedkwatar hukumar a sansanin alhazai na jahar.
      Sashen mahalarta taron NAHCON 
 Taron wanda aka dauki wasu 'yan awowi ana yin sa an tattauna muhimman batutuwan da suka hada da batun wa'adin karbar kudin ajiya daga maniyatan da suke da niyyar sabke farali, batun neman sanin yawan adadin kudin da za'a biya da sauran wasu batutuwan da suka shafi aikin. 
Idan za'a tuna, gwamnatin Jahar bisa jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda wanda ya sha alwashin ganin cewa, wannan aikin Hajji na 2024 maniyatan da suka fito daga ita har zasu yi aiki cikin jin dadi da walwala ta hanyar samar masu da ababen da zasu ji dadin su domin samun sukunin yin aikin Hajjin su cikin natsuwa. 
Kazalika, duk a bisa kokarin gwamnatin Jahar bisa jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda tuni ta sha karfin kusan kashi 80 cikin 100 na shirye-shiryen aikin Hajjin na 2024, abin da kawai ake jira shi ne, sanin tahakikanin abin da maniyatan zasu biya na wannan shekara wanda ake sa ran samun sauki ba kamar yadda wasu ke zato ba. 
Har'ila yau, duk a cikin shirin nemawa maniyatan na jahar Katsina sauki a wannan aiki wanda ya shigo a cikin wani yanayi matsin tattalin arziki da ya shafi duniya, shi kan shi Babban Daraktan hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama yayi kira ga a dubi batun canjin dala a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a kwanan tare da wata Æ™ungiya da sauran masu ruwa da tsakin. 
Shi dai wancan taro tare da ita NAHCON za'a ci gaba da yin shi a ranar 31 ga watan Disamba, 2023 kamar yadda sanarwar da Kakakin hukumar na Jahar Katsina Alhaji Badaru Bello Karofi ta sanar. Kazalika, daga cikin wadanda suka zauna don halartar wannan taro sun hada da Shugabam hukumar jin dadin alhazan Alhaji Kabir Bature sarkin Alhazai da wakilin majasalis dokokin jahar Katsina wanda ke shugabancin kwamitin majalisa mai kula da harkokin addini Honarabil Alhaji Umar Ali Bindawa. Daraktan kudi da na Gudanar da aikin na Hajji na daga cikin wadanda suka halarci taron. 

Post a Comment

Previous Post Next Post