AN DAKATAR DA SHUGABAN WATA MAKARANTA BISA ZARGIN CIN ZARAFIN WATA DALIBA A KATSINA

AN DAKATAR DA SHUGABAN WATA MAKARANTA BISA ZARGIN CIN ZARAFIN WATA DALIBA A KATSINA 

 Daga Kabir Ahmed S/Kuka

Bisa ga wani rahoto da ya fito daga karamar hukumar Dandume inda ake zargin shugaban wata makarantar sakandiren je-ka ka dawo na cin zarafin wata dalibar shi, Gwamnan Jahar Malam Umar Dikko Radda ya bayar da wani ummar akan lamarin. Gwamnan ya umarci Kwamishinan Ilmin bai É—aya na Jahar da ya dakatar da Malam Lawal Ibrahim nan take bisa wancan zargi na cin zarafin É—alibar sannan ya binciki lamarin. Shi dai Malam Lawal Ibrahim shi ne shugaban makarantar dake garin Dantankari dake cikin karamar hukumar ta Dandume sannan ya kaiwa Gwamnan sakamakon binciken
 Kazalika, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ta Katsina ya yi, 
Binciki wancan zargi da ake yiwa malamin. Har ila yau, ya binciki Jami'in yansanda(DPO) na karamar hukumar ta Dandume akan zargin gamsuwar shi akan neman  a yi sulhu da lamarin a lokacin da aka kai ma shi koke, shi ma a kai rahoto ga Gwamna.

Post a Comment

Previous Post Next Post