YAN ASALIN JAHAR KATSINA MAZAUNA JAMHURIYAR NIJER SUN YABA DA MATAKAN TSARON DA GWAMNA RADDA KE ƊAUKA

'YAN ASALIN JAHAR KATSINA MAZAUNA JAMHURIYAR NIJER SUN YABA DA MATAKAN TSARON DA GWAMNA RADDA KE ƊAUKA

Daga Kabir Ahmed S/Kuka a Niamey
Ƙungiyar 'yan asalin Jahar Katsina mazauna jamhuriyar wadda ke da hedkwata a birnin Yamai babban birnin ƙasar sun yaba da irin matakan tsaron da gwamnatin Jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda take ɗauka don kawo ƙarshen matsalar tsaron dake fuskantar Jahar Nuhu Muhammad wanda yayi magani a madadin ƙungiyar yace, irin labaran da suke samu a yanzu yana faranta masu rai saɓanin baya da kullum suke cikin zullumi. "A baya muna zullumin jin ina da ina waɗannan 'yan ta'adda suka kai hari a cikin ƙauyukan mu, wace irin ɓarna suka yi da sauran su, amma yanzu irin labaran da muke samu musamman akan yadda waɗannan jami'an tsaron da Gwamna ya ƙaddamar gaskiya muna jin irin namijin ƙoƙarin da suke yi wajen zaƙulo irin waɗannan mugayen mutane masu sayar da jinanen 'yan uwan su akan kuɗin da basu naira dubu ashirin ba".
Kamar yadda shi ma Malam Hamisu yace, "farko muna ganin laifin gwamnati na gaza yin komi, domin ko shi ma Gwamnan na yanzu farko mun ɗauka duk labarin siyasa ne don neman goyon baya, amma yanzu mun tabbatar da duk wani abin da ya faɗi zai yi na kawo ƙarshen matsalar tsaron da gaske yake yi. Za mu iya cewa, ya zama Zakaran gwajin dafi domin shi ne gwamna ɗaya tilo kuma na farko a arewa maso yamma da ya kafa irin wannan jami'an tsaro kuma aka fiddo su daga yankunan da abin ya fi shafa domin sun fi kowa sanin lungu da saƙo na maɓoyar waɗannan miyagu. Babban abin da yafi ƙara bamu natsuwa shi ne, irin yadda suke kama waɗannan baragunbin al'ummar masu baiwa 'yan bindigar bayanai ta yadda suke shigowa suna ta'adi". 'Yan ƙungiyar waɗanda suka nuna damuwar su akan irin yadda masu shigowa Najeriya musamman masu zuwa Jahar Kano suke ƙauracewa biyowa ta yankin Jibiya daga Maradi ko ta yankin Faskari ga masu biyowa ta yankin Sokoto zuwa Zamfara su faɗo Gusau don saboda farmakin  'yan bindigar dajin, sun gwamce su bi ta Damagaram wasu su shiga ta Jahar Jigawa ko kuma ta yankin Daura shi ma a tsorace. Wannan zagayen kamar yadda suka ce, ba ƙaramar asarar kasuwanci ba ce ga Jahar.
Kamar yadda suka ce, duk da cewa, suna zaune a wajen ƙasar ne amma kowane lokaci suna goyon bayan gwamnatin da irin tsare-tsaren da take ɗauak har da batun yadda ake aza masu ilmi a wajen harkokin gwamnati. Masu magana da yawon 'yan ƙungiyar sun yi kira ga sauran jami'an gwamnatin da cewa su ji tsoron Allah a wajen sabke nauyin dake bisa wuyan su. Su sani shi Gwamna yayi na shi, saura ya rage wajen su. Ƙarshe sun bayar da shawarar cewa, inda hali, cikin naɗe-naɗen da yake yi, ya naɗa wani jami'i ko mashawarci wanda zai riƙa basu bayanan halin da ake ciki na tafiyar gwamnatin shi sannan ita kuma gwamnatin ta san irin halin da suke ciki, sannan koda wani abu ya taso na bayar da wata gudunmuwa ko shawara ko kuma goyon baya. Wanda za'a naɗan ya zamo mazaunin cikin Jahar ne wanda yake mu'amulla da 'yan jahar mazauna waɗannan ƙasashe na Afirka ta Yamma ba wai Nijer kawai ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post