NUJ TA TAYA KANWAN KATSINA MURNAR CIKA SHEKARU 23 A BISA MULKI

NUJ TA TAYA KANWAN KATSINA MURNAR CIKA SHEKARU 23 A BISA MULKI
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
 
 Majalisar Æ™ungiyar 'yan jaridu ta Jahar Katsina NUJ ta taya Kanwan Katsina Hakimin Ƙetare Alhaji Usman Bello ƘanÆ™ara mni murna yayin da yake cika shekaru ashirin da uku a kan karagar mulki
A cewar shugaban Æ™ungiyar Alhaji Tukur Hassan Dan Ali, " a matsayinmu na 'yan jarida da masu sa ido na al'umma, mun fahimci a cikin shekaru ashirin da uku na shugabancin gargajiya na Alhaji  Usman Bello Kankara an samu nasarori bisa la'akari da ci gaban da aka samu a yankin a cikin wadannan shekaru. Hakimim wanda kuma yake tsohon Kwanturola ne wanda yayi ritaya a Hukumar Kwastam ta Najeriya, mun fahimci cewa Alhaji Bello wanda ake kira da U.K Bello ya yi amfani da hikimar sa, Æ™warewar shi a aiki da kuma bin horon da ya samu gami da sadaukarwa ga al'ummar da yake yi wa hidima". 
 Dan Ali ya Æ™ara da cewa, Hakimin na Ƙetare Alhaji  U.K Bello za a iya kwatanta shi da mutun ne wanda yake mu'amula da mafi yawan Kafofin watsa labarai na ciki da wajen Jahar Katsina kasancewar shi na tsohon Kakakin ita waccan hukuma ta Kwastan. Bisa la'akari da wadannan da ma wasu halaye na Alh.  Usman Bello Kankara yasa  ’Yan jarida a Jihar Katsina suna alfahari da kasancewa a ko da yaushe tare da shi Kanwan na Katsina bisa kyakkwar mu'amula gami da irin shawarwari tare da gudunmuwa don tafiyar da aikin mu na jarida a duk lokacin da muka tuntube shi ba tare da gajiyawa ba, inji shugaban Æ™ungiyar ta NUJ na jaha. 
Ƙarshe Æ™ungiyar tayi mashi fatan alheri da kuma ci gaba da samun nasara a bisa jagorancin da yake yi a sauran shekaru masu zuwa nan gaba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post