Katsina PWB : ZAMU YI AIKI KAFAƊA DA KAFAƊA DA KU - ED Dankama

Katsina PWB : ZAMU YI AIKI KAFAƊA DA KAFAƊA DA KU - ED Dankama

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
 A ranar Alhamishin jiya ce sabon Babban Daraktan hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama ya karbi ragamar jagorancin hukumar daga Daraktan sashen mulki na hukumar Alhaji Sada Salisu Ruma a hedkwatar hukumar dake bisa titin zuwa Daura a garin Katsina. Alhaji Yunusa Dankama ya canjin Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ne wanda ya riƙe hukumar tun a farkon shekarar 2020 wanda a halin yanzu ya samu wani wurin aikin. Bayan yiwa sabon Babban Daraktan murna tare da maraba, Daraktan sashen mulkin ya tamƙawa Babban Daraktan dukkan takardun da ya karɓa daga tsohon Babban Daraktan Nuhu Kuki a lokacin da shi sabon Babban Daraktan yake ƙasa mai tsarki don yin aikin Umra.
Alhaji Sada Ruma ya shaidawa Babban Daraktan cewa, mahukuntan hukumar sun yi aiki tare da tsohon Babban Daraktan bakin rai bakin fama. Kazalika, shi ma zasu bashi duk wani haɗin kai a lokacin gudanar da aiki domin ganin cewa ya samu duk wata nasarar da yake bukata a lokacin da yake wannan jagoranci.
A nashi ɓangaren, bayan yayi nuna farin cikin shi akan yadda aka tarbe shi da kuma irin yadda aka hannata mashi ragamar mulkin hukumar, Alhaji Yunusa Dankama ya tabbatar masu da cewa, zasu ci gaba aiki kafaɗa da kafaɗa da ma'aikatan wannan hukuma domin ganin cewa an gudu tare an tsira tare. Ya kuma ƙara jaddada neman haɗin kan duk wani ma'aikacin hukumar tare da sauran masu ruwa da tsaki akan su ci gaba da bashi goyon baya don ganin cewa ana aiwatar da aiyukan hukumar kamar yadda doka ta tanada.
Alhaji Yunusa Dankama ya miƙa godiyar ga Gwamna Malam Umar Dikko Radda bisa ga wannan matsayi da ya bashi na jagorancin wannan hukuma. Ya ce, da ikon Allah zai tafiyar da wannan hukuma ba tare da kawo wani bambanci ko son kai ba kasancewar hukuma ce wadda ta shafi aiyukan ibada.
Shi dai Alhaji Yunusa Dankama ba bako ba ne a wajen tafiyar da sha'anin mulki domin ya riƙe shugabancin karamar hukumar Kaita, yayi Ɗan majalisa da sauran rike wasu mukamai. Ta fuskar tafiyar da jama'a kuma ba bako ne saboda gogaggen ɗan siyasa ne. 

Post a Comment

Previous Post Next Post