Katsina BA MU YARDA DA CIN ZARAFIN MATA 'YAN JARIDA - NAWOJ

Katsina BA MU YARDA DA CIN ZARAFIN MATA 'YAN JARIDA - NAWOJ

A wata takardar sanarwa da ta fitar a cikin satin nan, ƙungiyar mata 'yan jaridu ta ƙasa NAWOJ reshen Jahar Katsina, ta yi kira tare da yin gargaɗi da kakkausar murya akan cewa ba zata zura ido ko lamunta akan yiwa mata 'yan jarida cin zarafi ko wani tozarci ba a duk inda suka samu kan su don gudanar da aikin su. Ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabar ta Kwamared Hannutu Mohammed ta sanar da haka ta hannun Sakatariyar ƙungiyar Faith Awa Moji wadda suka rabawa kafafen yaɗa labarai takardar ƙungiyar akan wancan batun.
Kamar yadda shugabar ƙungiyar ta ce, su ma mata 'yan jaridu mutane kuma ma'aikata ne kamar sauran dangin su maza waɗanda suke aiki kafaɗa da kafaɗa a duk inda aka je aiki, don haka babu dalilin nuna masu wata wariya. Shugabar wadda ta nuna fushin ƙungiyar su a fili tace, irin abin da aka yiwa wata ma'aikaciyar jarida a gidan rediyon Jahar Katsina abin takaici da Allah wadai ne. Kwamared Hannatu ta ƙara da cewar, korar da Manajan gidan rediyon yayi Fauziya Mamman Dawai ya saba dokar aiki kuma cin zarafi ne da nuna zalunci a fili, domin kamar yadda tace, irin rahotannin da suka samu, rashin samun wata biyan bukata da shi manajan yayi ne ga ita Fauziya yasa yayi amfani da kujerar shi ya kore ta bayan kuma dalilin da yasa ya yi amfani da matakin da yake gani laifi ne wanda zai iya ɗaukar hukunci ba abu ne mai ƙarfin da zai sa hakan ta faru ba sai fa inda wata manufa ko wani abu ɓoyayye.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, shi manajan ya ɗauki wannan hukunci ne bisa dalilin cewa ya kira wani taro a gidan amma ita bata halarci taron ba, bayan kuma tana cikin gidan amma tana can wajen aiwatar da aikinta na gabatar da labarai. Har'ila yau, rahoton ya ce, Daraktan da take ƙarƙashin shi, ya rubuta sunayen su inda ya baiyana suna aiki a daidai wannan lokacin don haka ba zamu samu damar halartar wannan taro ba. Har ila yau, ance wani babba daga sashen da take, wato, sashen labarai da al'amurran yau da kullum sai da ya sake bayar da sanarwar cewa suna cikin aikin yin labarai ba zasu samu damar halartaar taron ba. Amma kamar yadda majiya mai tushe tace, shi manajan yayi watsi da wannan sanarwa da kuma uzurin da aka gabatar mashi inda yace, ya ƙyale biyu amma ita ya kore ta, har ma aka ce yayi wani lafazi na shaguɓe, "na kore ki sai kuma inga yanzu wanda ya isa ya sake maido ki".
Kamar yadda rahotanni suke yawo an tabbatar da cewa, a ranar 8 ga watan Nuwamba 2023 kaɗai ya sa an ba mutun 18 takardar tuhuma (query) akan rashin ganin su zaune acikin ofisoshin su bayan kuma mafi yawan su ba masu aikin zama ofis ba ne duk kuwa da rubuta sunayen su a littafin zuwa aiki. Wani abin da ya ƙara bada mamaki shi ne, hatta da wanda ya gaishe shi a matsayin shi na shugaba sai da yasa aka bashi wannan takarda. Kamar yadda NAWOJ ta koka, tana ganin wannan wani salo ne na shugaban don firgita matan dake aiki ƙarƙashin shi ta yadda zasu ba bori kai ya hau a duk lokacin da ya kaɗa garayar.
A hannu guda, ƙungiyar ta jinjinawa Gwamna Radda akan irin yadda ya ɗauki matakin gaugawa na kafa kwamiti don bincikar yadda lamarin yake. Kazalika, ƙungiyar ta bukaci a faɗaɗa bincike a sauran wuraren da shi wannan manaja yayi aiki don tabbatar da gaskiyar zargin da ake yi ma shi musamman akan mu'amullar da wasu aiyuka maras kyau. Shugabar ƙungiyar ta ƙara da cewa, ba zasu yi ƙasa a guiwa ba na ganin cewa sun ƙwato haƙƙin Fauziya wadd take aikin wucin-gadi a gidan rediyon tare da sauran duk wata mace 'yar jaridar da aka tozarta ko aka tauye mata haƙƙi. A ƙarshe sun yi fatan Gwamna zai ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan shi wannan manaja da ma sauran shugabanni masu ɗabi'a irin ta shi

Post a Comment

Previous Post Next Post