BA A SAN WADANDA SUKA KASHE HAMZA ZAKKA BA - Al'umma
Al'ummar garin Zakka dake karamar hukumar Safana sun bayyana cewa mutanen da suka kashe tsohon shugaban riko Alh. Hamza Abdullahi har yanzu ba a tantance ko su wanene ba.
Idan dai za a iya tunawa, an tsinci gawar tsohon Shugaban riko da wasu mutane biyu da ake zargi da hadin kai ko kuma ba da labari ga ‘yan bindigar daji ne kimanin makonni biyu da suka gabata a wajen garin Zakka.
Wani dan jarida da ya ziyarci kauyen ya lura cewa yayin da iyalan marigayi Shugaban riko ke neman Adalci, su kuwa yawancin jama'ar yankin na cikin yanayi mai kyau.
A wata hira da aka yi da wani dan asalin garin Zakka Alh. Sani Sada ya ce kusan kullum al’ummar yankin na fuskantar hare-hare da dama wadanda a cewarsa watakila ba su da alaka da kashe wadanda ake zargi da kai labari. Alh. Sani Sada wanda ya zubar da hawaye a lokacin da yake zantawa da dan jaridan da ya ziyarci unguwar, ya tuno yadda wasu ‘yan bindiga suka kai wa gidansa hari da karfi da yaji suka tafi tare da dan shi da misalin karfe tara na safe.
Har ila yau, wani limami a garin Zakka, Liman Sahalu Lawal ya ce sabanin zargin da iyalan marigayi Shugaban riko suka yi, shi (Limamin) ya jagoranci sallar jana’izar marigayi Hamza. A daya bangare Iimamin ya ce sun taru ne a unguwar Sha’iskawa da ke kauyen domin yi wa Gwamna Dikko Umar Radda addu’a.
Wani dan garin Malam Yakubu Abubakar ya ce “matasa a yankin na ba da cikakken goyon bayan bullo da jami’an tsaro na al'umma da gwamnatin jihar Katsina ta yi a yanzu.