ABUBUWA 7 DA SUKA HANA CI GABAN KASUWANCI A JAHAR KATSINA - Abdurrashid Ɗanbedi

ABUBUWA 7 DA SUKA HANA CI GABAN KASUWANCI A JAHAR KATSINA - Abdurrashid Ɗanbedi

Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Idan aka waiwayi tarihi, Katsina ce cibiyar kasuwanci a arewancin ƙasar nan tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka. Katsina har ila yau,ita ce babbar mahadar yada zago daga fataken dake fitowa daga yankin Sahara ta arewa har ya zuwa wasu yankuna na ƙasashen larabawa. Wasu 'yan kasuwar baya-baya da za'a iya tunawa sun haɗa da Hajiya Ɓaika, Alhaji Abu Kyahi wanda shi ne ɗan kasuwa na farko da ya fara sayen mota a lokacin mulkin Sarki Dikko.
Masu nazari ko tarihi sunce harkokin kasuwanci sun fara ja baya tun lokacin da turawan mulkin mallaka suka fara shigowa Katsinar inda suka nemi korar larabawa da buzayen da tuni suka zama jiki a cikin al'umma. Ance bayan ba ni gishiri in baka mandar da suka fara yi ta hanyar kawo kayan ƙyale-ƙyali irin su madubi, hoda da sauran irin su gami da kayan sawa wanda suka saɓawa al'ada da addini, an samu rashin jituwa tsakanin su da sarakuna da malaman wancan lokaci. Kamar yadda aka ce, zowar su ta ƙarshe ita ce wadda suka yi da jirgi mai sabkar Angulu irin na wancan zamani wanda rashin sanin shi ya ƙara haifar da wata matsalar, tilas suka bar Katsina zuwa Kano. Daga wannan lokaci suka mayar da harkokin su zuwa Kano ta amfani da jirgin. Wannan ne yasa daga bisani aka riƙa zuwa Kanon ana sayo kayan da suka kawo. Hakan ne kuma ya janyo Kano ta mamaye harkokin kasuwanci a arewa.
To abin tambaya anan shi ne, shin za'a ce tun tsawon wancan lokaci har zuwa yau abin da ke bibiyar Katsina kenan a batun koma bayan kasuwancin ko akwai wasu dalilan daban? Alhaji Abdurrashid Salisu Ɗanbedi, tsohon shugaban 'yan kasuwa da ƙananan masana'antu na Jahar Katsina ya ce, a wannan iskan mai bugawa ba shi ne dalilin ba domin an cigaba da harkokin kasuwanci a fadin jahar ba wai garin na Katsina kawai ba. Sai daina cewar shi akwai wasu dalilai har guda bakwai(7)da suka kawo koma bayan harkokin kasuwancin.
"Babban dalili wanda kuma yake shi ne na farko harkar matsalar tsaro. Malam an hana noma wanda kuwa shi ne kan gaba wajen tafiyar da harkokin kasuwanci a mu nan yankin. Yanzu subi ana cikin farkon kaka ne, amma ina abin da ke yawo a kasuwanni na sayarwa balle harma ayi tunanin sayen wasu kayayyakin. 'Yan bindigar daji sun hana komi a wannan fanni. Wannan shi ne dalilin farko. Dalili na biyu shi ne, rashin tallafi daga gwamnati zuwa ga 'yan kasuwar kai tsaye. Yana da kyau ace gwamnati ta riƙa tallafawa su 'yan kasuwar koda kuwa ta tsaya masu ne ga bankuna su basu rancen jarin da zasu haɓaka kasuwancin nasu, amma maimakon hakan, sai wasu su je su karɓi bashin da sunan 'yan kasuwar ba kuma don suyi kasuwancin ba".
Alhaji Abdurrashid Ɗanbedi ya ƙara da cewa, raahin gaiyato wasu kamfanoni daga waje don zuba jari ko kafa masana'antu a jahar na daga cikin dalilan rashin ci gaban harkar kasuwancin. Kazalika, tsohon shugaban ƙungiyar 'yan kasuwan da masana'antun yace, hatta da bayar da tallafin bashin yin noma an siyasantar da shi a Jahar wanda ake ci da sunan manoman amma kuma basu ganin ko sisi balle su yi noman, amma kuma sai ace ana bin su bashin wasu ma har a fara cire masu kudi a bankin in suna da asusun ajiyar ba kuma tare da cewar sune suka yi amfani da kudin ba sunayen su kawai aka yi amfani da shi.
Hatta da su kan su 'yan kasuwar Ɗanbedi bai bar su ba a wajen hana kasuwa ci gaba a jahar ta Katsina wanda shi ne ya ce abu na biyar. "Mu kan mu 'yan kasuwar da zarar ka ji ance a zo a haɗa kai, to batun yadda za'a ƙara farashin kaya ne wanda kuma ƙarshe zalunci ne ke shiga. Duk yadda muka sayo kaya da arha, muddin muka ji wani ɗan labari na ƙarin farashi walau daga kamrani ko wani sashe na hukuma, nan take mu zamu canza ko da kuwa can ba'a canza ba. In an canza aka rago ba mu ragowar sai muce ai mai tsada muka sayo bayan can baya mai arhar ne muka ƙarawa kuɗin.
Alhaji Abdurrashid ya ci gaba da cewa, matsala ta bakwai ita ce tsame hannun gwamnati baki ɗaya daga harkokin kasuwanci inda ta bar kowa yayi yadda yake so maimakon ta shigo ka'in da na'in wanda hakan ne zai bayar da damar ɗaukar wani mataki a wajen fara shi da kuma kawo hanyoyin ci gaban kasuwancin. A ƙarshe sai ya bayar da shawarar yadda za'a magance duk waɗancan matsaloli ta hanyar inganta tsaro da kuma shigar gwamnati don tsayawa 'yan kasuwar, wato, giranto wajen neman bashin inganta kasuwancin. 

Post a Comment

Previous Post Next Post