KatsinaZaben 2023 - JAM'IYAR APC ZATA AMSO KUJERUN TA DA AKA DAUKE A JAHAR KATSINA - Muntari Lawal

KatsinaZaben 2023 - JAM'IYAR APC ZATA AMSO KUJERUN TA DA AKA DAUKE A JAHAR KATSINA - Muntari Lawal
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Tsohon Babban Sakataren gidan gwamnatin Jahar Katsina kuma tsohon Shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin, kazalika, tsohon Sakataren gwamnatin Jahar ta Katsina Alhaji Muntari Lawal yace, da yardar Allah sauran kujerun jam'iyar APC da aka dauke a zaben 2023 da aka yi jam'iyar zata amso abin ta daga wadanda suka yi masu sama da fadi ta hanyar shari'a kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokokin hukumar zabe suka tanadar. 
Alhaji Muntari Lawal ya fadi haka ne a lokacin da yake taya zababben Dan majalisar Wakilai na Tarayya daga shiyyar Kankiya Kusada Honarabil Abubakar Yahaya Kusada da takwaran sa na Katsina Honarabil Sani Danlami murnar basu kujerun su da kotun daukaka karar zabe tayi a wannan sati da ya gabata. Har'ila yau, Tsohon Sakataren gwamnatin Jahar ta Katsina ya taya Alhaji Salisu Yusuf Majigiri murnar na jam'iyar PDP wanda ya kira da sunan É—an-uwa murnar bashi kujerar shi wadda yayi takara kuma ya ci zaben. 
Alhaji Muntari har wayau, yayi fatan sake amso kurajen su biyu, wato, na Honarabil Zakka da kuma Honarabil Tafoki inda yace, su ma da yardar Allah kotun zata amso su daga inda aka kai domin mika su ga masu su na halaliya. Kazalika, tsohon Sakataren ya taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da sauran gwamnonin jam'iyar su ta APC murna cika kwanaki 100 na gwaji acikin nasara, inda yace babu ko tantama zasu yi aiki tukuru domin kawo cigaba. 
Indai za'a iya tunawa, Alhaji Muntari Lawal yana daga cikin manyan 'yan siyasar da kasa ke alfahari da su ba wai a matakin jaha kawai ba. Shi ne wanda ya jagoranci yaÆ™in neman zaben Masari a zaben 2015 da kuma 2019 inda ya rike mukamin Babban Daraktan yakin neman zaben. 
Alhaji Muntari Lawal bai tsaya a batun kawo cigaba a harkokin siyasa domin a shekarar 2019 yayi Amirul Hajji na Jahar Katsina a inda ya zamo na farko da aka lambar yabo daga wata kungiyar yada labaran aikin Hajji hadin guiwa da hukumar Aiyukan Hajji ta kasa NAHCON a matsayin Amirul Hajjin da yayi zarra. Har'ila yau, shi ne wanda ya maido da martabar hukumar jin dadin alhazai ta jahar har ta dawo cikin haiyacinta, abin da ya janyo har a aikin Hajjin 2022 da aka yi Jahar ta Katsina ta sake samun wasu lambobin yabon wanda har a lokacin tsohon Gwamnan Jahar Rt. Aminu Ballo Masari ba'a bar shi a baya wajen wannan karramawa a matsyin gwamnan da yayi fice a wajen kyautatawa mahajjata. 

Post a Comment

Previous Post Next Post