Katsina PWB - LAMBAR YABO KARO NA 5 TABBAS JUYI TARA SAI WAKE
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Batun gudanar da hidimomin maniyatan aikin Hajji har zuwa su zamo alhazai, hukumar Jin dadin Alhazai ta Jahar Katsina na a sahun gaba wajen ganin tayi iya kokarinta na ganin maniyatan Jahar basu samu wata matsala ba tun daga gida har zuwa ƙasa mai tsarki wanda ya haɗa har da batun dawowar su cikin ƙoshin lafiya kamar yadda suka tafi.
Tun bayan ɓullar cutar Korona wadda ta hadda dakatar da komi a fadin duniya wanda shi kan shi aikin Hajjin ba'a bar shi a baya ba, hukumomin wasu jihohi sun yi shiru dangane da tafiyar da harkokin su, amma a Jahar Katsina ba haka abin ya zamo ba. A daidai wannan lokaci ne bayan rushe shugabancin hukumar a shekarar ta 2019 aka kawo Alhaji Sulemain Nuhu Kuki don jagorantar hukumar duk kuwa da halin da ake ciki na rashin tabbas ga aiyukan na Hajji. Wannan matsala bata sa shi Babban Daraktan hukumar Alhaji Kuki yin shirun jiran tsammani ba, sai yayi ta kokarin kawo wasu 'yan gyare-gyare a hukumar inda kuma ya samu cikakken hadin kan sauran jami'an hukumar da ya taras don ganin cewa, kambin da hukumar ta fara rikewa a 2019 na samar da jajirtaccen Amirul Hajji Alhaji Muntari Lawal wanda hakan yasa wata ƙungiyar 'yan jaridu mai zaman kanta Independent Hajj Reports hadin guiwa da hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON tare da sa hannun jakadancin Saudiya dake Najeriya suka bada lambar yabo ta samun gwarzon Amirul Hajj na 2019.
Shekaru biyu cur aka yi ba tare da aiwatar da aikin Hajjin ba daga wasu kasashen na Duniya.
Shekarar 2022 ita ce shekarar farko da shi Babban Daraktan hukumar Jin dadin alhazan na Jahar Katsina Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ya fara jagorantar aikin Hajjin daga Jahar ta Katsina. A wannan aikin na 2022, Kuki ya janyowa jahar lambobin yabo har guda uku.
Daya daga cikin lambobin harda wadda bankin Keystone ya baiwa hukumar bisa yabawa da irin yadda hukumar ta aiwatar da harkokin maniyatan ba tare da samun wata matsala ba. Lamba ta biyu ita ce ta yabo akan yadda hukumar ta samar da masabkai ga maniyatan jahar a can garin Makka.
Masabkan da maniyatan suka yaba da su da kuma irin yadda aka kula da su. Sai lamba ta uku, wadda aka baiwa Gwamna Aminu Bello Masari akan irin yadda Jahar ta zamo zakaran gwajin dafi a wajen samarwa maniyatan na wannan lokacin dukkan abubuwan da suke bukata, musamman abinci wanda shi ne babban abinda kowane maniyaci yake bukata. Ga masabkai kusa da Harami, sannan ga ciyarwa.
A wannan shekara ta 2023, kowa yasan irin matsalolin da aka fuskanta a wannan aiki, musamman a zaman Muna da aka yi. Hakan bai sa hukumar jin dadin alhazan ta jahar Katsina tayi ƙasa a guiwa ba wajen ganin tayi bakin iyawarta don ragewa mahajjatan matsalolin da wasu suka samu musamman na masabki da abinci. Wannan matsala bisa ga binciken da ASKGLOC NEWS suka yi ya samo asali daga hukumomi a can Saudiya da kuma ita hukumar aikin ta ƙasa wato NAHCON. Matsalolin da suka fito daga Saudiya sune, na bayar da adadin inda za'a kafa hemomi daidai da na shekarar 2022 wanda mahajjatan shekarar 2023 sun lunka wadanda suka je wancan aiki. Matsalar NAHCON da bata bi abin ba tun kafin lokacin aikin don tabbatar da halin da ake ciki. Bugu da ƙari, akwai matsalar Tukaru. Wannan matsala ta Tukaru kusan ta mamaye mafin yawan masabkan alhazan a zaman Muna, kuma sune suka mamaye kusan duk wani abu na mahajjatan wannan shekara.
Duk da samun wadannan manyan matsalolin, hukumar jin dadin alhazan ta Jahar Katsina sai da tayi kokarin tsamo wadannan Tukaru daga cikin mahajjatanta, ta fitar da su. Sannan ta bullo da wani salo na bayar da abinci ga mahajjatanta har zuwa lokacin da aka gama wannan zama basu ƙara fuskantar matsalar wajen kwana ko abinci ba.
Har ila yau, wani abin da masu lura suka lura da shi daga wannan hukuma shi ne, irin yadda tun daga gida aka rika yiwa maniyata taron bita da fadakarwa, abinda yayi tasiri matuka wanda ya janyo mahajjatan Jahar Katsina suka sha bamban a wajen ɗa'a da kiyaye doka. Babu wani sashe na masu ruwa da tsaki na aikin hajjin da basu aiwatar da aikin da ya rataya a wuyan su ba, kama daga malamai, wakillan ƙananan hukumomi, kwamitin aikin Hajjin ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin kuma Magajin garin Katsina Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir da sauran su.
Duba da irin jajirtacewar hukumar yasa a wannan aikin Hajji na 2023 ta sake samun lambar yabo daga waccan ƙungiya akan irin yadda hukumar bisa jagorancin shi Babban Daraktan Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ta bayarda da kulawa tare da ganin mahajjatan jahar sun gudanar da aikin su daidai gami da bin kadin abubuwa a tsanake. Daraktan sashen kudi na hukumar Alhaji Sagir Inde Sarkin Musawan Katsina shi ne wanda ya karbi wannan lamba a madadin hukumar wadda aka bayar a ranar 21 ga watan Satumba, 2023 a babban birnin tarayya Abuja.