JARIRIN DA AKA KASHE MAHAIFIN SHI A RANAR BIKIN SUNAN SHI YA SAMU TALLAFIN NAIRA MILYAN GUDA DAGA GWAMNATIN JAHAR KATSINA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Gwamnatin Jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Dikko Radda ta baiwa iyalan jami'an tsaro 'yan sintiri da suka rasa rayukan su ko raununa wajen faɗa da ɓarayin daji masu garkuwa da mutane su 33 inda aka fidda naira milyan 20. Waɗannan kuɗaɗe naira milyan 20 za'a raba su ga iyalan mutanen su 33 inda kowane zai samu naira dubu ɗari biyar. Daga cikin waɗanda zasu karɓi wannan tallafi har da matar da aka kashe mijinta a ranar da ake sunan jaririn da suka haifa.
Kamar yadda Mai baiwa Gwamnan Shawara ta fannin bayar da tallafi ga waɗanda iftila'in 'yan bindigar ya shafa Alhaji Sa'adu Ibrahim Ɗanja ya shaida a wajen taron bayar da wannan tallafi ga waɗanda abin ya shafa. Ya ƙara da cewa, tun daga watan Yuli na wannan shekara har zuwa yau, duk wanda wannan iftila'in ya shafa gwamnati zata cigaba da tallafa masu walau ta magani ko wani abin dabam. "Yanzu haka, akwai mutane 20 da suke karɓar magani kyauta a asibitin ƙashi da kuma asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake nan cikin garin Katsina sakamakon raunukan da suka samu. Akwai soja guda da wani jami'in da Gwamna ne zai bayyana abin da zai ba iyalan su", inji shi.
Kwamandan rundurun 'yan sintiri na Jahar Katsina Malam Salisu Rabo ya baiyana yawan mutanen da 'yan bindigar da suka kashe daga ƙananan hukumomin da abin ya shafa waɗanda suka kai adadin mutane 33 da wasu waɗanda yace ba zai iya tunawa ba, kuma dukkan su ba a lokacin wannan gwamnati ta Malam Umar Dikko Radda abin ya faru gare su ba, amma ya ɗauki wannan nauyi.
A nashi jawabin Gwamnan Jahar wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin Jahar Barista Abdullahi Garba Faskari ya ce, tun farkon jawabin Gwamnan tun yana yawon yaƙin neman zaɓe ya sha nanata cewar batun sha'anin tsaro ne ke kan gaba a wajen mulkin shi in har Allah ya bashi mulkin Jahar, kuma in har zai kashe kuɗaɗen jahar don tabbatar da tsaro to a shirye yake akan hakan. Ga shi kuma jama'a na shaidawa domin tun kafin ya fara aiwatar da wannan aiki sai da ya tara duk wasu masu ruwa da tsaki akan harkar tsaron don neman shawara kuma ana cigaba da aiwatarwa da kuma ci gaba da amsar wasu shawarwarin daga jama'a. Sakataren ya baiyana cewa, Gwamna Malam Umar ya bayar da naira milyan guda ga iyalan wani jami'in tsaron soja da ya rasa ran shi a ranar da ake bikin sunan ɗan shi.
Malam Garba Musa ɗaya daga cikin waɗanda suka samu raunuka yayi godiya a madadin sauran waɗanda suka karɓi wannan tallafi, inda ya tabbatarwa gwamnati ci gaba da aiki tare da bada goyon baya don ganin an kawo ƙarshen aiyukan ta'addanci a faɗin Jahar baki ɗaya.