Hajj 2023 - GWAMNA RADDA YA CANCANCI YABO - Darakta Kuki

Hajj 2023 - GWAMNA RADDA YA CANCANCI YABO - Darakta Kuki

Daga Kabir Ahmed S/Kuka 


Aikin Hajjin 2023 da ya gabata anyi shi a tsakanin gwamnatoci biyu a Jahar Katsina, gwamnati mai barin gado ta Gwamna Aminu Masari wadda ita ce ta shirya aikin da kuma sabuwar gwamnatin Malam Umar Dikko Radda wadda ita ce ta aiwatar da aiki. Har'ila yau, gwamnatin Malam Umar Radda ta aiwatar da aikin acikin wani yanayi na tsadar rayuwa da kuma iftila'in yaƙin ƙasar Sudan wanda ya tilastawa jiragen dake tashi daga filin sabka da tashin jiragen sama na Umaru Musa 'Yar'aduwa yin zagayen don kaucewa ƙasar ta Sudan, lamarin da ya janyo ƙarin farashin kuɗin kujerar zuwa aikin Hajjin. Dalilin da yasa har ita hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON ta ta rage yawan kuɗin guzurin da ake baiyar inda aka cire dalar Amurka 100 daga cikin 800 da ake bayarwa.
Ganin haka, yasa gwamnatin Jahar ta Katsina ƙarƙashin shi Gwamna Malam Umar ta yi wani tsarin na ko ta kwana don gudun kada maniyatan Jahar su fuskanci wasu manyan matsaloli. Kamar yadda Babban Daraktan hukumar Jin dadin alhazan na Jahar Katsina Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ya shaidawa wakilin ASKGLOC NEWS a wata hirar da suka yi, "mun cigaba da magana da juna a tsakanin mu a duk lokacin da muka ji wani abu ya ta so, wanda kuma in na neman yarda ce daga gwamnatin babu bata lokaci Mai girma Gwamna zai amince da shi. Kamar yadda shi Gwamna Malam Dikko Umar Radda yake yawan nanatawa cewa, ba zaiyi wasa da wannan aiki na ibada ba da sauran duk wani lamari da ya shafi addini.
"Wani misalin da zan kawo anan shi ne, a lokacin da muka isa garin Makka, mun taras an roshe inda muka saba kama ofis, amma bawan Allah nan ina bugo mashi cewar ga halin da ake ciki, nan take ya amince da fidda wasu milyoyin don tunkarar wannan matsalar ta ofis. Da yake Allah yaga abin da ke cikin zuciyar shi na alheri ne, ƙarshe muka maidowa gwamnati da waɗannan kudade domin mun samu wata mafita ga lamarin. Sannan duk wanda ya je aikin Hajjin 2023 yaga irin matsalolin da aka fuskanta a zaman Mina na ƙarancin masabki da kuma abinci. Ba hakkin gwamnatin Jaha ba ne anan amma mu a Jahar Katsina rana guda kawai muka fuskanci wadannan matsaloli biyu domin Maigirma Gwamna da yaji wannan matsala kuma ya gani da idon sa tunda duk shekara sai ya je, nan take yace mani ga yadda za'ayi kuma Allah cikin ikon shi sai muka zamo abin koyi ga wasu jihohin.
Darakta Kuki ya ci gaba da cewa, duk zaman da mahajjatan Jahar Katsina suka yi a garin Makka na tsawon wadannan kwanaki kusan 40 ko fiye, babu alhajin da zaice yayi kukan yunwa ko an bashi abincin da bai saba da shi ba. "Sannan wani abin da ya ƙara burge duk wani mahajji na Jahar Katsina shi ne, goron salla na Riyal 300 da ya ba mahajjatan Jahar. Kuma Jahar ce kawai ta bayar da wadannan makudan kudade. Kun ji dai ku 'yan jarida yadda wasu jihohin suka bayar. Wasu ma Riyal 50 suka bada kuma ba kowa ya samu ba. Kuma kuwa anan jahar har ma sai da muka maido kusan na mutun 40 da basu samu damar zuwa. Ka kauga ace, an bayar da irin wadannan kudin har ma da ƙarin na yawan adadin da aka bada ai ba karamin tallafi ba ne. Riyal 300 sau dubu 4 da wasu daruruwa ya kake gani?"
Alhaji Suleiman yace, su matsayin su na jagororin alhazan jahar a hukumance baya ga yabo da godiya babu abin da zasu yiwa wannan gwamnati ta Malam Umar Radda." Irin jajircewar da gwamnati tayi akan wannan aiki duk kuwa da tsadar abubuwa wanda ya shafi duniya baki daya, hakan ya kara sanya har lambar yabo muka samu ta fannin Æ™oÆ™ari, fadakarwa da kuma tallafawa mahajjata", inji shi. 

Post a Comment

Previous Post Next Post