'YAN APC SUN KARRAMA MATAIMAKIN KAKAKIN MAJALISAR DOKOKI A KATSINA

'YAN APC SUN KARRAMA MATAIMAKIN KAKAKIN MAJALISAR DOKOKI A KATSINA 
Kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Safana a jihar Katsina, ta karrama Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Honorabul .Abduljalal Haruna Runka AJ da lambar yabo.
           Honorabil AbdulJalal Runka
 Taron bikin karramawar wanda ya hada da fitattun ‘ya’yan karamar hukumar Safana maza da mata, ya gudana ne a sakatariyar karamar hukumar.
 Da yake jawabi a wajen taron shugaban kwamitin, Alhaji Aliyu Sa'id ya bayyana cewa an karrama Abduljalal Haruna AJ ne saboda irin kyawawan nasarorin da ya samu a fagen siyasar yankin. Ya kara da cewa, mataimakin shugaban majalisar da ya kasance na farko a tarihi daga yankin kuma na farko da ya samu nasarar lashe zaben majalisar dokokin jihar har sau uku a jere.  .
 Alhaji Aliyu ya bayyana cewa Abduljalal Runka, ya dauki nauyin kudirori da dama a zauren majalisar, wanda ya kai ga gina titin Dutsinma-Babban Duhu-Kukar Samu da dai sauran ayyuka abin yabawa.
       Honarabil Muhammad Kabir Umar
 Shi kuwa shugaban karamar hukumar Safana Honorabul Muhammad Kabir Umar ya bayyana wanda aka karrama a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda ya jajirce wajen tafiyar da harkokin siyasa a yankin. Shugaban ya kara da cewa, Mataimakin Kakakin Majalisar matashin dan siyasa mai kishin kasa, mai aminci da da’a.
 Su kuwa sarakunan yankin, Yariman Katsina Hakimin Safana Alhaji Sada Rufa'i da Gatarin Katsina Hakimin Zakka Alhaji Sani Zakka sun yi kira ga sauran 'ya'yan yankin maza da mata da su cigaba da ba Mataimakin Kakakin goyon baya domin ganin ya ci gaba da kawo aiyukan alheri. 
 A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Dokokin jihar Alhaji Nasir Yahaya Daura, ya yabawa al’ummar da suka yi bikin karrama dansu cikin yanayi mai dadi. Kakakin majalisar wanda ya bayyana Abduljalal Runka AJ a matsayin abokin aiki kuma makusancinsa, ya ce majalisar za ta ci gaba da samar da dokoki don amfanin yankin da jihar baki daya.
Da yake mayar da martani, wanda aka karraman Abduljalal Runka, ya yaba da wannan karramawar, inda ya tabbatar da cewa ba zai kyale su a haka nan ba.
 Ya kuma yabawa 'yan majalisar yakin neman zaben na jam’iyyar APC ta da ta karbe shi, da kuma yadda suke ci gaba da fafutukar ciyar da jami'iyar a gaba musamman ta hanyar shawo kan abin da ke ci mata tuwo a kwarya.

Post a Comment

Previous Post Next Post