Yaƙi da Nijer : INGIZA MAI KANTU RUWA A KE YIWA NAJERIYA - Ɗanƙaura

Yaƙi da Nijer : INGIZA MAI KANTU RUWA A KE YIWA NAJERIYA  - Ɗanƙaura

Wani matashin malami kuma manazarcin al'amurran yau da kullum a Jahar Katsina ta tarayyar Najeriya Malam Bishir Ɗankaura yayi fashin baƙi akan wani yunƙurin kai farmakin yaƙi ga ƙasar Nijer da ake ta yamaɗiɗi na cewar ƙasar Najeriya zata kai da sunan ƙungiyar ECOWAS. Manazarci yayi bayani kamar haka:
"Abin da ke faruwa a ƙasar Niger, abubuwa ne dake ta canza salo. Da farko wasu na ganin Faransa ce ta kitsa juyin mulkin saboda ƙudirin Bazoum akan samarwa Niger cikakken 'yanci.
Daga baya kuma sai aka fahimci Sojojin da suka yi juyin mulkin, ba su tare Faransar.
Duk waɗannan zagaye zagaye, aje a dawo, Makircin Kacokam Nigeria aka nufo da shi domin a watsa ƙasar.
Hawan Ahmed Bola Tinubu shugabancin Nigeria ko kwanaki 100 bai cika , aka zaɓe shi shugaban ECOWAS, saboda wata boyayyen manufa da makirci.
Dalili kuwa shi ne, ta ya ya sabon shugaba da zai mulki ƙasa mai cike da tarin matsaloli irin Nigeria a bashi shugabancin ECOWAS daga hawan sa bayan ga sauran shuwagabannin ƙasashen Afrika ta Yamma da suka daɗe, kuma suke da gogewa?

"MAKIRCIN a nan shi ne, tun bayan juyin mulki da aka yi, ECOWAS ta umarci Sojojin Niger su mayar da mulki ga farar hula, ko kuma su ɗauki matakan Soji. 
Daga baya kuma ƙasar Nigeria , ta zama ita ke kan gaba wajen zaƙewa da nuna isa a madadin ECOWAS. Har aka ce wai Sojojin Nigeria sun ce Umarni kawai suke jira su afkawa Niger.
Wannan ingiza-mai-kantu ruwa da ake wa Nigeria babbar barazana ce ga ƙasashen biyu. Domin ƙasashe ne da guda, ba ta yi sai da guda. 
Tinubu ba ɗan Arewa ba ne, balle ya san irin danganta da kuma tasirin da Ƙasar Niger take da shi a Arewa.
Akwai Alamomin Tambayoyi sosai. Misali... 
- Ƙashashe nawa ne akai juyin mulki ba'a za'a yaƙe su ba sai Niger ?
- Shuwagabannin ECOWAS nawa akai, ba'a san su ba har suka ajiye sai yanzu a TUNIBU ?
- Me yasa ECOWAS ba ta damuwa da Ta'addanci, da Kuma matsin Rayuwar da ake fuskanta a ƙasashen biyu? 
Idan har wannan makirci ya yi nasara, Nigeria ta afkawa Niger tabbas abin ba zai yi kyau ba. Domin za a rusa al'umma mai al'adu da addini kusan iri ɗaya.
Garuruwan dake makwabtaka da Nigeria za su shiga cikin bala'i. Domin garuruwan za su zama yankin Sojojin ECOWAS da Sojojin Ƙasashen Waje.
Sannan akwai yiyuwar Sojojin Niger su riƙa mayar da murtani. Misali Gwamnan Maradi na Soja bai zai ƙyale Sojojin Nigeria salin-alin ba su yi abin da suke so, haka na Zinder da Tawa da Dosso wadanda dukkan su suna iyaka da wasu jihohin Najeriya. 
Daga ƙarshe za a yi ƙazamin faɗa, domin kowanne ɓangare zai nemi taimakon ƙasashen wajen. Misali Niger ta nemi taimakon Rasha ko Korea. Ita kuma Nigeria ta nemi taimakon Amurka da Faransa. 
Wannan faɗan zai ƙara farraƙa haɗin kan ƙasashen Afrika musamman na Afirka ta Yamma. Yankin zai zama wani filin daga in da Sojojin Ƙasashen Waje za su ci karen su ba babbaka. Kamar yadda aka yi a Saliyo, Somaliya, Libya da Ƙasar Afrika ta tsakiya,
A Nigeria ta Arewa, Talauci zai ƙaru, Talakawa za su ƙara shiga matsi, 'yan gudun hijira da makamai za su yawaita. Mutane za su fara bore, za a koma mai karfi shi ne ke da iko. 

Yan Kudu za su buƙaci a raba ƙasar, saboda faɗan bai shafe su ba. Tun da abin da suke so ke nan. Daga ƙarshen ƙarshe a raba ƙasar bayan an mayar da Arewa Kufai kuma sansanin Makamai da Ta'addanci.
 Ku sani.. Abin da ake shirin yi wa Niger, kamar kai ne da gidan ka, amma ace ga Lokacin da za ka riƙa dawowa gida, ga abin da za ka riƙa ci, ga lokacin da za ka riƙa share shi, ga lokacin da za ka gyara shi.
Ƙasar Niger ƙasa mai 'yanci, suna da haƙƙin da za su zaɓa wa ƙasarsu makoma. 
Ku sani Niger ta yi wa Nigeria hallaci a lokuta da dama. Domin ko a lokacin yaƙin Biyafara, ta ƙasar ce ake shigo mana da abinci da makaman da ake ba Sojoji.
Muna roƙon Allah ya kawo ƙarshen abin nan, masu ƙulla Makirci ga ƙasashen biyu, da ma na Afrika baki ɗaya, ya koma masu".

Post a Comment

Previous Post Next Post