Da dumi-dumi - ZA'A GURFANAR DA HAMBARARREN SHUGABAN KASAR NIJER GABAN KULIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Hukumomin soja a Jamhuriyar Nijar da ake kira CNSP a takaice sun ce zasu gufarnar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum wanda suka yiwa juyin mulki a 'yan kwanakin nan a gaban kuliya manta saboda bisa zargin shi da cin amanar kasa.
Sabbin hukumomin sojan kasar sun sanar da aniyarsu ta gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da kuma wasu da suka kira ‘yan ta’addan da ake zarginsu da cin amanar kasa da kuma zagon kasa ga tsaron cikin gida da wajen kasar ta Nijar. Dangane da musanyar da Bazoum ya yi da ‘yan kasar da shugabannin kasashen waje da jami’an kungiyoyin kasa da kasa, sojojin da ke kan madafun iko sun ce sun tattara dukkan shaidu da abubuwan da suka dace akan wannan tuhuma da suke yi.
Idan za'a tuna, sojojin karkashin jagorancin babban jagoran tsaro na fadar ta shugaban kasa Laftanar Janar Abdoulrahame Tchiani Umar sun hanbarar da shugaba Baozoun a 'yan kwanakin da suka gabata bisa zargin yin ko in kula da matsalar tsaro da kasar take fuskanta gami da almubarraci da dukiyar kasa, sannan da kuma aniyarsu ta yin hannu riga da kasar Faransa wadda ta yiwa Kasar mulkin mallaka kuma ta dawo tana yi masu bita da kulli.