Da dumi-dumi - NIJER TA YANKE HULDA DA NAJERIYA DA WASU KASASHEN UKU

Da dumi-dumi - NIJER TA YANKE HULDA DA NAJERIYA DA WASU KASASHEN UKU
Bayan juyin mulkin Sojoji a kasar Nijer inda suka tunbuke gwamnatin Muhammad Bazoum na fara hula, kungiyar ECOWAS ta baiwa sojojin wa'adin sati guda da su mayar da mulki ga Bazoum ko kuma su fuskanci matakin sojojin hada ka. 
Bayan wannan sanarwa ta ECOWAS, shugaban Najeriya wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS ya tura wata tawaga zuwa Nijer don ganawa da sojojin da suka yi juyin mulkin don tattauna mafita ga abin da ka iya biyo baya. Tawagar karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya Abdussalam Abubakar wadda tayi kwana biyu a kasar, amma a karshe haÆ™ar bata cimma ruwa ba. Sakamakon abin da ya biyo baya shine, Æ™asar ta Nijer sai ta bayar da sanarwar yanke hulda da Najeriya da Togo dq Amurka da kuma Æ™asar Faransa wadda tayi masu mulkin mallaka, kamar yadda jaridar nan ta "Dailytrust" ta ruwaito. Yanzu abin da za'a zura ido a gani shi ne, me zai biyo bayan yanke wannan hulda wadda ba'a baiyana ko ta wane bangare aka yanke ta ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post