YADDA MAHAJJATAN JAHAR KATSINA JIRGI NA 6 YA SABKA

YADDA MAHAJJATAN JAHAR KATSINA JIRGI NA 6 YA SABKA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka 
Mahajjatan Jahar Katsina da suka hada daga shiyyoyin Katsina, Kankiya, Dutsinma da sauran wasu sun sabka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'adua dauke da mahajjata 420.
Jirgin Max Air Boeing 777 5N-BBN ya sabka da misalin karfe 11 da minti 39 na rana. Acikin shi akwai wasu daga cikin malamai da 'yankwamitin aikin hajji na Jahar Katsina.
Wasu daga cikin wadanda wakilin ASKGLOC NEWS ya zanta da su sun nuna farin cikin su akan yadda suka gudanar da wannan aikin ibada cikin nasara ba tare da fuskantar wasu manyan matsaloli ba.
Wasu daga cikin malaman da muka zanta da su musamman akan yadda mahajjatan suka karbi wa'azi da kuma taron bitar da aka yi masu, Malam Hamza Safana yace, "alhazan jahar Katsina sun cancanci yabo ta irin yadda suka nuna ladabi da biyayya tare da tsare dokoki. Sun yi amfani da koyarwar da aka yi masu sosai domin da mutun yaga wani abin da zai shige mashi duhu babu bata lokaci zai nemi masana. Su kan su hukumar alhazan tayi rawar gani". 
Shi ma Malam Shehu Abubakar Adoro, daya daga cikin membobin kwamitin aikin Hajjin na Jahar ta Katsina ya baiyana farin cikin shi akan irin yadda mahajjatan suka jajirce a wajen bin hudubar da aka yi masu musamman wajen batun yin canjin kudi da sayayyar barkatai da sauran irin su.
Kazalika, Malama Ummul Khairi Ibrahim Kankara, daya da cikin mata masu wa'azi tace, tabbas wannan aiki mata sun yi iyakar yin su wajen ganin sunyi aikin kamar yadda ya kamata. "Yar matsalar da aka samu ita ce a ranar yin jifar farko inda aka samu wasu matan sun bace, amma Allah cikin ikon shi basu tagaiyara ba aka gano su, kuma daga wannan babu wata matsalar da sashen mata ya samu. Sannan mu kan mu idan akwai wani abin da ya shige mana duhu muna tuntubar su Hajiya Binta Mai larabci da su Hajiya Halima domin neman karin haske kuma suna ba mu.
Mafi yawan wadanda muka tuntuba suna nuna farin cikin su da gamsuwa da irin yadda hukumar jin dadin alhazan bisa jagorancin Babban Daraktan Alhaji Sulemain Nuhu Kuki da gwamnatin Jahar Katsina Æ™arÆ™ashin jagoranci Gwamna Malam Umaru Dikko Radda da sauran masu ruwa da tsaki akan aikin ta irin karramawa da mutuntawar da aka yi ta hanyar karbar duk wani koke ko ganin basu aikata wani abin da zai zubar da mutuncin jahar ba. 

Post a Comment

Previous Post Next Post