JIRGI NA 2 NA MAHAJJATAN JAHAR KATSINA YA TA SO DAGA JEDDA
Jirgi na biyu na Mahajjatan Jahar Katsina ya taso daga filin jirgi na Sarki Abdul Aziz dake Jedda zowa Katsina. Jirgin na Max Air 5N-ADM ya ta so da karfe 11 da minti 20 na daren larabar nan dauke da mahajjata 530 da suka fito daga ragowar shiyyar Mani, sai na Malumfashi da kuma wasu daga shiyyar Funtuwa.
Kamar yadda ASKGLOC NEWS suka yi magana da Babban Daraktan hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Katsina Alhaji Sulemain Nuhu Kuki ta wayar salula ya nuna farin cikin shi akan irin yadda aikin ke tafiya cikin nasara kamar yadda aka tsara.
Kazalika, Kuki ya jinjinawa mahajjatan akan irin yadda suka yi juriya tare da nuna goyon bayansu ta bin doka da oda akan rashin kwaso su a lokacin da mafi yawan suka yi zato bayan kammala aikin ibadar.
Har ila yau, Babban Daraktan ya yabawa abokan aikin shi tare da sauran masu ruwa da tsaki akan ganin anyi nasarar yin wannan aiki musamman shi Amirul Hajj, tsohon Kakakin majalisar dokokin jahar Katsina, Honarabil Tasi'u Maigari Zango, shugaban kwamitin aikin Hajji daga majalisar dokokin jaha Honarabil Mustaga Jibiya, shugaban kwamitin aikin Hajjin Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir wanda yake kuma Magajin Garin Katsina tare da sauran duk masu ruwa da tsaki akan irin yadda suka bayar da tasu gudunmuwar musamman ita gwamnatin Jahar ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda wadda yace basu da abin da zasu ce akan irin gudunmuwar da ta basu sai godiya.
Tuni dai jirgin farko dauke da mahajjata 547 suka sadu da iyalansu bayan sun sabka lafiya da misalin karfe 7 da minti 37 na yammacin wannan laraba.
Shi kan shi wannan jirgi na biyu ana sa ran zai sabka a filin sabka da tashin jirage na kasa da kasa na Umaru Musa 'Yar'aduwa dake cikin garin Katsina a tsakanin a wajen asubahin wayewar garin alhamis cikin yardar Allah