Hajj 2023 - JAHAR KATSINA TA KAMMALA AIKIN HAJJIN TA LAFIYA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
Kamar sauran wasu jihohin na Najeriya, Jahar Katsina ta kammala aikin Hajjin 2023 lafiya ba tare da fuskantar wasu manyan matsaloli ba sai na É—an abin da ba'a rasa ba. Jahar wadda ta kai mahajjata sama da dubu 4 don sabke wannan farali duk kuwa da tashin kwabron zabon da kujerar aikin wannan kujera tayi a fadin duniya baki daya.
Jirgi na 9 wanda kuma shine jirgi na karshe wanda ya kwaso ragowar alhazan sama da dari 4 sun iso gida da wajen asubahin ranar asabar 29 ga watan Yuli na 2023 a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar'adua dake cikin garin Katsina. Jirgin na kamfanin Max Air kirar Boeing 747 mai lamba 5N-ADM VM2032, ya dauko duk wasu masu ruwa da tsaki na aikin tun daga Amirul Hajj Honarabil Tasi'u Maigari Zango, shugaban kwamitin aikin Hajjin kakauma Magajin garin Katsina Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir, Babban Daraktan hukumar Jin dadin alhazan Alhaji Sulemain Nuhu Kuki sauran su.
To shin Jahar Katsina ta sake kafa abubuwan tarihi kamar yadda ta saba dangane da aikin Hajji ko akwai wani kalubalen da ta fuskanta a hukumance? Yaya mahajjatan Jahar suka aiwatar tare da yadda suka kalli aikin na wannan shekara ta 2023. Wadannan tambayoyin da wasu makamantan su ASKGLOC NEWS zata yi kokarin kawo maku amsoshin su a rahoto na musamman akan aikin Hajjin 2023
Yayi kyau. Muna jiran jin abubuwan alheri
ReplyDelete