Hajj 2023 - DA ALAMU SAI MAHAJJATAN NAJERIYA SUN SAKE KOMAWA MADINA
Alamu na nuni da cewar akwai yuwuwar sai mahajjatan Najeriya da suka sabke farali a wannan shekara ta 2023 sai sun sake komawa garin Madina a karo na biyu kafin kwaso su zuwa gida. Rahotannin da suke shigo mana a yanzu na baiyana cewar hukumomin Saudiya sun fito da wani sabon tsari na kwasar mahajjatan daga filin jirgin Madina maimakon Jedda da aka saba. Hukumomin sun ce sun dauki wannam tsari ne sanadiyar cinkoso da shi filin jirgin na Abdul Aziz yake fuskanta a halin yanzu.
Mahajjatan da abin ya shafa sun hada da wadanda kamfanonin jiragen sama na Aero Air, Air Peace, Max Air da Azman suka yi jigilar su don zuwa ƙasar. Fara jin wannan labari yasa wasu mahajjatan sun fara nuna damuwar su musamman ganin irin yadda zasu sake yin wasu awowin da zasu kai 7 zuwa 8 daga Makka zuwa Madinar kuma acikin mota sannan kuma su sake yin wasu awowin acikin jirgi kafin su iso gida wanda suna ganin hakan zai galabaitar su, wasu ma ƙila abin ya zamo masu sanadiyar kamuwa da wata cutar bama kamar ta ƙafafu duba da irin yadda ba'a dade da kammala aikin Hajjin ba wanda kashi 95 daga cikin shi duk a tafiya ƙasa ne.
Sai dai wata majiya ta kusa da hukumar dake kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON ta nuna damuwar ta akan wannan canji da su hukumomi a ƙasar ta Saudiyya suka ɗauka akan wannan tsari wanda ya shafi Najeriya. Majiyar tace, tuni su NAHCON suka rubuta takardar ƙorafi akan wannan inda suke neman a mayar da su inda aka saba, wato, daga Makka zuwa Jedda wadda tafiyar bata wuce ta awa guda da 'yan mintoci ba,wanda kuma suke fatan samun biyan bukata akan hakan.
Shi dai wannan aikin Hajji na bana ya ci karo da ƙalubale iri-iri tunda farkon sa, musamman ga al'ummar Najeriya. Tun a wajen biyan kuɗin ajiya maniyatan suka fara samun wannan ƙalubale na tashi gwabron zabon da kudin kujerar suka yi. Bayan tsallake wannan siradi na farko sai kuma ga batun ɓarkewar yaƙi na ƙasar Sudan wanda hakan ya tilasts dole sai anyi wani dogon zagaye kafin a shiga ƙasar da Saudiya. A can baya ana shiga ta ƙasar Chadi ne zuwa Sudan ɗin a tsallake ruwa sai Saudiyya, tafiyar da bata wuce awa 4 da wasu mintoci ba, amma sanadin yaƙin yasa aka canza hanya daga Chadi zuwa Libiya zuwa ƙasar Egypt sannan a tsallake ruwa zuwa ƙasar ta Saudiyya. Wannan zagaye har ila yau, baya ga daukar wasu awowi abin ya sake haifar da wani ƙalubalen ga maniyatan domin hakan yasa an janye masu dala 100 daga cikin kudin guzurin su. Maimakon dala 800 da ake bayarwa sai ta dawo 700 inda aka yi amfani da dala 100 domin yin ciko ga kamfanonin jiragen da suka yi jigilar saboda koken da suka yi na tsadar mai da kuma ƙarin nisan tafiyar.
Kazalika, wani babban ƙalubalen da wannan aikin Hajji yayi kicibis da shi shine, na masabkai a Mina. Sai da hukumomi a Saudiyyar suka ƙarawa mahajjatan Najeriya tentuna a ƙalla duba 10 amma duk da haka basu isa ba, sai dai aka riƙa gwamawa. Hatta da batun ƙarancin abinci wannan aiki na bana bai barshi a baya ba. Sai kuma wani babban ƙalubalen da ASKGLOC NEWS suka samo rahotansa na batun kula da lafiyar mahajjata. Duk koke-koken da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi suke yiwa ita NAHCON akan wannan fanni, a wannan aikin Hajjin na 2023 abin ya ƙara fitowa fili akan waccan matsala ta ƙin sakarwa jihohi mara su kula da mahajjatan su ta wannan fanni. Rahotanni sun nuna cewa, lallai an kai kayan aiki da ma'aikatan lafiyar, sai dai babbar matsalar ita ce cinkoso da dogon layi, wanda maras lafiyar dake son a duba shi a ƙalla yana iya kwashe sama da 8 ko 10 bai samun ganin jami'an kiwon lafiyar ba don jin abin da ya same shi koda kuwa wace irin rashin lafiya yake fama da ita. Fitar da wuri guda ace nan za'a duba masu lalurar rashin lafiya daga cikin mutanen da suka kusa milyan guda a irin wannan yanayi ba ƙaramar matsala ba ce.
Anan, ASKGLOC NEWS na ganin cewa, yana da kyau ita hukumar kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON ta duba wannan lamari da kyau ta bar jihohi su riƙa kula da mutanen su ta fuskar kiwon lafiya kamar yadda ake yi da.