GWAMNAN JAHAR KATSINA MALAM UMAR YA BAIWA MAHAJJA GORON SALLA
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A ranar wannan lahadin ce Gwamnan Jahar Katsina Malam Umar Umar Dikko Radda ya baiwa mahajjatan Jahar Katsina da suka haura dubu da wasu É—aruruwa goron salla na Riyal 300 kwatankwacin naira dubu 60 ga kowane mahajjaci domin samun saukin yin wasu hidimomin.
Amirul Hajji na wannan shekara kuma tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jahar Katsina ne Alhaji Tasi'u Maigari Zango ne ya sanar da mahajjatan a kowane gida da ya kai masu ziyara. Gwamnan ya ce, mahajjatan su yi amfani da abinda ke hannun su domin kada su shiga cikin wani hali musamman ta bangaren abinci da sauran su ganin irin yadda rayuwa ta yi tsada a ƙasar. Kazalika, Gwamna Malam Umar ya sake yin kira ga Mahajjatan da su cigaba da yiwa Jahar Katsina addu'o'in samun zaman lafiya da ƙaruwar arziki.
A nashi jawabin, Babban Daraktan hukumar Jin dadin alhazan na Jahar Katsina Alhaji Sulemain Nuhu Kuki godiya yayi ga mahajjatan akan irin yadda suka zamo masu ladabi da biyayya da hakuri tare da juriya musamman a zamansu na Mina wanda aka fuskanci wasu 'yan matsaloli amma mahajjatan suka jajirce, kamar yadda takardar sanarwar da fito daga ofishin Jami'in hulda da jama'a na hukumar Alhaji Bello Badaru Karofi ya sanyawa hannu.
Ko a wannan karon ma, za'a iya cewa, alhazan da suka fito daga jahar Katsina sun ƙara kafa wani tarihin na nuna zaman lafiya tare da bin dokokin gida da na can ƙasa mai tsarki, domin har ya zuwa rubuta wannan rahoto, babu wani bayanin da ya fito na yin bore ko wasu manyan korafe-korafe tun daga zaman su na Madina, Makka, Mina har dawowa garin Makka bayan kammala aikin Hajjin duk kuwa da cewa, baƙin zuwa aikin sun yawa