Da dumi-dumi - SAUDIYA TA AMINCE DA TASHIN ALHAZAN NAJERIYA DAGA JEDDA

Da dumi-dumi - SAUDIYA TA AMINCE DA TASHIN ALHAZAN NAJERIYA DAGA JEDDA

Labarin dake shigo mana a yanzu nan na cewa hukumar aiyukan Hajj da Umra ta ƙasar Saudiya ta amince da ci gaba da kwaso mahajjata daga filin jirgi na Abdul Aziz dake Jedda. 
Kamar yadda wani jami'in ɗaya daga cikin jiragen da suka yi jigilar mahajjatan wanda kuma jirgin kamfanin na daga cikin jirage 4 da wancan tsari na farko da kasar bayar da aiwatarwa ya shafa, wato, jirgin Max Air, jami'in yace, bayan sun yi taro da hukumar a jiya laraba, a yanzu wannan tsari ya shafi waɗanda suka je aikin ne ta jirgin yawo. Masu jirgin yawo ne zasu rika tasowa daga Madina, sauran mshajjata kuwa zasu taso ta inda aka saba, wato, Jedda. 
Indai za'a tuna, farko ƙasar ta Saudiya ta ce mahajjatan Najeriya da jiragen Aero Air, Air Peace, Max Air da kuma na Azman zasu kwaso mahajjatan ne daga filin jirgin Madina, tsarin da hukumar kula da aiyukan Hajji ta ƙasa NAHCON ta yi ƙorafi a kai. 

Post a Comment

Previous Post Next Post