Da dumi dumi MAHAJJATAN JAHAR KATSINA 547 SUN SABKA LAFIYA

Da dumi dumi MAHAJJATAN JAHAR KATSINA 547 SUN SABKA LAFIYA
Mahajjatan Jahar Katsina jirgin farko su 547 sun sabka lafiya a filin jirgi na Umaru. Musa Yar'adua dake cikin garin Katsina. S7n sabka da misalin karfe 7 da minti 37 na yammacin Larabar nan. Jirgin Max Air Boeing 747 5N-HMM ne ya kwaso mahajjatan daga Jedda da misalin karfe 2 da mintuna 47 na yamma. Mahajjatan shiyyar Daura ne jirgin ya kwaso.
Wani labarin, yayin da jirgi na farko ya sabka, jirgi na 2 na can yana shirye-shiryen tasowa da mahajjata 530 wadanda ake sa ran isowar da safiyar gobe. 

Post a Comment

Previous Post Next Post